Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zan Yi Don Iyayena Su Yarda Da Ni?

Me Zan Yi Don Iyayena Su Yarda Da Ni?

 Abin da ya kamata ka sani

 Kuna bukatar ku nuna ta ayyukanku cewa za a iya yarda da ku. Yin biyayya ga iyayenku yana nan ne kamar biyan bashi. Kuna bin iyayenku bashin yi musu biyayya, kuma da zarar kuna biyan bashin nan za su ci gaba ba ku rance ko kuma za ku ci gaba da samun karin ’yanci daga wurinsu. Amma idan kuna yin abubuwan da suke sa iyayenku kin yarda da ku, kada ku yi mamaki idan suka rage ba ku ‘rance.’

 Zai dauki lokaci kafin iyayenku su yarda da ku. Kuna bukatar ku nuna ta halayenku cewa kun manyanta kafin iyayenku su ba ku karin ’yanci.

 TARIHI: Wani matashi mai suna Craig ya ce: “A matsayin matashi, na san abubuwan da iyayena suke so in rika yi. Nakan nuna musu cewa ina yin abubuwan nan, amma a boye ina yin abin da nake so. Hakan ya sa ya yi wa iyayena wuya su yarda da ni. Da shigewar lokaci, na fahimci cewa idan ina so in sami ’yanci, ina bukatar in rika fadin gaskiya. Mutum yana bukatar ya rika fadin gaskiya idan yana so mutane su yarda da shi.”

 Abin da za ka iya yi

 Ka rika fadin gaskiya ko da hakan bai da sauki. Kowa yana yin kuskure amma idan kuka yi karya ko kuma kuka fadi rabin gaskiya don ku boye kuskurenku, hakan zai sa iyayenku su ki yarda da ku. Akasin haka, idan iyayenku suka san cewa ku masu fadin gaskiya ne hakan zai sa su ga cewa kun manyanta domin ba ku boye kuskurenku ba.

 Wata mai suna Anna ta ce: “Idan ka yi kuskure hakan ba zai hana iyayenka yarda da kai ba, amma idan ka yi kokarin boye kuskurenka hakan ne zai hana su yarda da ka.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nufinmu shi ne mu aikata abin da yake daidai cikin ayyukanmu duka.”—Ibraniyawa 13:18.

  •   Ka yi tunani a kan wannan: Idan iyayenka suka tambaye ka wurin da za ka je da kuma abin da za ka yi a wurin, kana fada musu gaskiya kuwa? Ko kuma idan iyayenka suka tambaye ka wurin da ka je da kuma abin da ka yi a wurin, kana boye wasu abubuwan da ka yi da suke so su sani?

 Ka nuna ka manyanta. Ka rika bin dukan dokokin da iyayenka suka kafa. Ka rika yin aikace-aikace a gida. Ka rika yin abu a kan lokaci. Ka rika yin aikin makaranta. Kada ka taka dokar iyayenka na hana fita.

 Wani mai suna Ryan ya ce: “Idan iyayenka suka amince ka fita yawo da abokanka kuma suka ce ka dawo gida karfe tara daidai, kada ka dawo gida karfe goma da rabi, domin idan ka yi haka, nan gaba ba za su amince ka fita yawo da abokanka ba!”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama ya kamata kowa ya dauki kayan kansa.”—Galatiyawa 6:5

  •   Ka yi tunani a kan wannan: Iyayenka sun san kana kammala aikace-aikacen gida a kan lokaci kuwa? Sun san ka da bin dokoki ko da ba ka son dokar?

 Ka yi hakuri. Idan iyayenka sun daina yarda da kai, zai dau lokaci kafin su soma yarda da ka. Ka kasance a shirye don ka jira lokacin.

 Wata mai suna Rachel ta ce: “Na damu sosai sa’ad da iyayena suka ki amincewa na rika yin wasu abubuwa duk da cewa shekaruna ya kai. Ban fahimci cewa idan mutum ya yi girma hakan ba ya nufin ya manyanta ba. Sai na gaya wa iyayena su ba ni damar nuna musu cewa na manyanta. Ya dauki lokaci, amma na yi nasara. Na koyi cewa yawan shekarun mutum ba shi ke sa a yarda da shi ba, amma ayyukansa ne zai sa a yi hakan.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku dinga auna kanku.”—2 Korintiyawa 13:5.

  •   Ka yi tunani a kan wannan: Idan kana so iyayenka su yarda da kai, wadanne abubuwa ne kake bukatar yi don ka tabbatar musu cewa za su iya yarda da kai?

 Shawara: Ka kafa makasudin yin abu a kan lokaci da bin dukan dokokin iyayenka har da na hana fita. Ka nuna wa iyayenka cewa wannan shi ne burinka, kuma ka tambaye su abin da suke bukatar ka rika yi don su yarda da kai. Bayan haka, ka yi kokarin bin shawarar Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Ai, abin da aka koya muku, shi ne ku yar da halin mutuntaka wanda kuke ciki a dā, halin da yake lalacewa saboda son abubuwa masu rudu.” (Afisawa 4:22) Da shigewar lokaci, iyayenka za su lura cewa kana samun ci gaba!