Koma ka ga abin da ke ciki

Yaya Yesu Ya Ce Mu Rika Bi da Mutane?

Yaya Yesu Ya Ce Mu Rika Bi da Mutane?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A hudubarsa na kan dutse, Yesu ya ce: “Duk abin da kuke so mutane su yi muku sai ku ma ku yi musu.” (Matiyu 7:12; Luka 6:31) Littafin nan Encyclopedia of Philosophy kuma ya ce: “Ka yi wa mutane abin da za ka so su yi maka.”

 Mene ne maꞌanar abin da Yesu ya ce?

 Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu rika bi da mutane yadda muke so su bi da mu. Alal misali, yawancin mutane suna so a girmama su, a bi da su a hankali kuma a nuna musu kauna. Hakazalika, zai dace mu rika yi wa mutane ‘abin da muke so su yi mana.’​—Luka 6:31.

 Me ya sa bin shawarar zai amfane mu?

 Shawarar nan da Yesu ya bayar za ta taimaka mana a kusan dukan yanayoyi. Alal misali, za ta . . .

  •   Karfafa zaman aure.​—Afisawa 5:​28, 33.

  •   Taimaka wa iyaye su tarbiyyartar da yaransu da kyau.​—Afisawa 6:4.

  •   Sa mu zauna lafiya da abokai da makwabta da kuma mutanen da muke aiki tare da su.​—Karin Magana 3:​27, 28; Kolosiyawa 3:13.

 Kaꞌidar da ke wannan shawarar da Yesu ya bayar daya ne da wadda ke Tsohon Alkawari. Shi ya sa Yesu ya ce shi ne manufar “Koyarwar Musa [wato littattafai biyar na farkon Littafi Mai Tsarki] da ta annabawa [littattafan da annabawa suka rubuta ke nan].” (Matiyu 7:12) Hakan ya nuna cewa shawarar na dauke da abin da aka nanata a Tsohon Alkawari cewa: mu kaunaci kowa.​—Romawa 13:​8-10.

 Yesu ya ba da shawarar don mu sami wani abu a wurin wasu mutane ne?

 Aꞌa. Ya mai da hankali a kan bayarwa ne. Saꞌad da Yesu ya ba da wannan shawara, ya yi magana ne game da yadda za mu bi da mutane gabaki daya har da makiyanmu. (Luka 6:​27-31, 35) Saboda haka, Yesu yana karfafa mutane su rika yi wa dukan mutane alheri.

 Ta yaya za mu bi shawarar?

  1.  1. Kada ka kasance da halin ‘ba ruwana.’ Ka rika lura da abin da ke faruwa da mutane da ke kusa da kai. Alal misali, kana iya ganin wani da yake fama da kaya da yawa ko ka ji game da rashin lafiyar makwabcinka ko kuma ka lura cewa wani abokin aikinka ba ya farin ciki. Idan kai mai “kula da wadansu” ne za ka nemi zarafi ka fadi ko kuma ka yi wani abin da zai taimaka wa mutane.​—Filibiyawa 2:4.

  2.  2. Ka zama mai tausayi. Ka yi kokari ka rika tunanin yadda mutumin da kake tausayawa yake ji. Yaya za ka ji idan kana cikin irin wannan yanayin? (Romawa 12:15) Idan ka yi kokari ka fahimci yadda mutane suke ji, za ka so ka taimaka musu.

  3.  3. Ka yi tunani matakin da za ka dauka idan da bukata. Ka tuna cewa mutane sun bambanta. Abin da wasu za su so a yi musu ba zai zama daya da abin da za ka so a yi maka ba. Don haka, a cikin abubuwan da za ka iya yi, ka zabi abin da kake gani za su fi so.​—1 Korintiyawa 10:24.