Koma ka ga abin da ke ciki

Allah Ne Ya Halicci Iblis?

Allah Ne Ya Halicci Iblis?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah bai halicci Iblis ba. Maimakon haka, ya halicci wani da ya mai da kansa Iblis. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah: “Aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, mara-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:3-5) Wannan ayar ta nuna cewa lokacin da Allah ya halicci malaꞌikan nan da a yau ya zama Shaidan Iblis, shi cikakke ne, wato kamiltacce ne, mai adalci kuma. Yana ɗaya daga cikin mala’iku ’ya’yan Allah.

 A Yohanna 8:44, Yesu ya ce Iblis “ba ya tsaya a kan gaskiya ba,” wato akwai lokacin da Shaiɗan ya yi gaskiya kuma bai yi laifi ba.

 Amma, kamar sauran halittun Jehobah masu basira, mala’ikan nan da ya zama Shaiɗan yana da ’yancin zaɓa tsakanin nagarta da mugunta. Ya mai da kansa Shaiɗan, wato, “Ɗan adawa” ta wurin matakin da ya ɗauka na yin hamayya da Allah kuma ya zuga ma’aurata na farko wato Adamu da Hauwa’u, su bi shi.—Farawa 3:1-5; Ru’ya ta Yohanna 12:9.