Ya Kamata Mu Yi Bauta wa Siffofi?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A’a bai kamata ba. New Catholic Encyclopedia ya kwatanta dokoki da Allah ya ba wa al’ummar Isra’ila haka: “A cikin nassosi da yawa babu wani tabbaci na cewa an hada bautar gaskiya na Allah da siffofi ba.” Ka bincika wadannan ayoyi na Littafi Mai Tsarki:
“Ba za ka misalta wata kira, ko surar abin da ke cikin sama daga bisa, ko abin da ke cikin duniya daga kasa, ko kuwa abin da ke cikin ruwa daga karkashin kasa: ba za ka yi sujada garesu ba, ba kuwa za ka bauta musu ba: gama ni Ubangiji Allahnka Allah mai-kishi ne.” (Fitowa 20:4, 5) Da yake Allah “mai-kishi ne,” ba ya farin ciki sa’ad da muka yi wa siffofi, hotuna, gumaka, ko alamu yabo ba.
“Ba ni kuwa bada daukakata ga wani, yabona kuma ga sifofi sassakaku.” (Ishaya 42:8) Allah ba ya karban sujjada da ake masa ta wurin siffofi ba. Sa’ad da wasu Isra’ilawa suka nemi su bauta masa ta wurin dan maraki, sai Allah ya ce: “Mutane ne masu zunubi.”—Fitowa 32:7-9, juyin Easy-to-Read.
“Bai kamata mu zaci Allantaka tana kama da zinariya, ko azurfa, ko dutse, abin da a kan sassaka ta wurin sana’ar mutum da dabarassa.” (Ayyukan Manzanni 17:29) Littafi Mai Tsarki ya ce, Kiristoci ‘bisa ga bangaskiya suke tafiya, ba bisa ga gani ba’ wannan dabam yake da bautar da arna suke yi da suke amfani da siffofi “sassaka ta wurin sana’ar mutum da dabarassa.”—2 Korintiyawa 5:7.
“Ku tsare kanku daga gumaka.” (1 Yohanna 5:21) Sau da sau a duk dokoki da aka ba wa Isra’ila da kuma Kiristoci, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa bautar Allah da ake yi ta wurin siffofi da alamu kage ne.