A Wace Hanya ce Hadayar Yesu Ta Zama “Abin Fansar Mutane da Yawa”?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Ta wajen hadayar Yesu ce Allah zai ceci ’yan Adam daga zunubi da kuma mutuwa. Littafi Mai Tsarki ya kira jinin Yesu abin fansa. (Afisawa 1:7; 1 Bitrus 1:18, 19) Shi ya sa Yesu ya ce ya zo domin ya “ba da ransa ... abin fansar mutane da yawa.”—Matta 20:28.
Me ya sa ake bukatar fansa don “mutane da yawa”?
An halicci mutum na farko, wato, Adamu babu zunubi. Da Adamu bai yi wa Allah rashin biyayya ba, da ya rayu har abada. (Farawa 3:17-19) Ya haifi ’ya’yansa cikin zunubi. (Romawa 5:12) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Adamu ya sayar da kansa da ’ya’yansa zuwa bauta ga zunubi da kuma mutuwa. (Romawa 7:14) Adamu da ’ya’yansa ba za su iya maido da abin da Adamu ya watsar ba domin dukansu sun zama ajizai.—Zabura 49:7, 8.
Allah ya ji tausayin ’ya’yan Adamu. (Yohanna 3:16) Amma duk da haka, Allah ba zai mance da zunubin haka kawai ba, domin shi mai adalci ne. (Zabura 89:14; Romawa 3:23-26) Allah yana kaunar ’yan Adam sosai, saboda haka, ya tanadar da abin da zai sa ya gafarta zunubansu gaba daya. (Romawa 5:6-8) Fansa ita ce wannan tanadin.
Ta yaya ake amfani da fansar?
A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai abubuwa uku da “fansa” ta kunsa:
Biya.—Littafin Lissafi 3:46, 47.
’Yanci.—Fitowa 21:30.
Samun abin da ya yi daidai da darajar abin da ake fansa. a
Ka yi la’akari da yadda wadannan abubuwa uku suka shafi hadayar fansa da Yesu Kristi ya yi.
Biya. Littafi Mai Tsarki ya ce an ‘sayi’ Kiristoci “da tamani” sosai. (1 Korintiyawa 6:20; 7:23) Abin da aka yi amfani da shi wajen sayensu shi ne jinin Yesu, wanda Yesu ya yi amfani da shi ya ‘sayi wa Allah mutane daga cikin kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma, iri-iri.’—Ru’ya ta Yohanna 5:8, 9.
’Yanci. Hadayar Yesu tana “’yantar” da mu daga zunubi.—1 Korintiyawa 1:30; Kolosiyawa 1:14; Ibraniyawa 9:15, Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.
Daidaituwa. Hadayar Yesu ta yi daidai da kamiltaccen rai da Adamu ya yi banza da shi. (1 Korintiyawa 15:21, 22, 45, 46) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kamar yadda masu dumbun yawa suka zama masu zunubi ta rashin biyayyar mutum daya [Adamu], haka kuma ta biyayyar mutum daya [Yesu Kristi] za a mai da masu dumbun yawa masu adalci.” (Romawa 5:19, Littafi Mai Tsarki) Wannan ya bayyana yadda mutuwar mutum daya yake fansar da masu zunubi da yawa. Babu shakka, hadayar Yesu fansa ce “daidaitacciya domin mutane duka,” wato, dukan wadanda suke kokarin su amfana daga wannan fansar.—1 Timotawus 2:5, 6, New World Translation.
a A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmomi na asali da ake amfani da su a madadin “fansa” suna nufin abu mai tamani da aka biya domin ’yantar da wani abu. Alal misali, kalmar Ibrananci da ake ce da ita ka·pharʹ tana nufin a shafe abu. Sau da yawa, yana nufin a shafe zunubi. (Zabura 65:3) Wata kalma kuma ita ce koʹpher, wadda take nufin abin da aka biya don a sami ’yanci. (Fitowa 21:30) Hakazalika, kalmar Helenanci lyʹtron, wadda ake fassara ta zuwa “fansa” tana nufin “abin da aka biya don a fanshi wani abu.” (Matta 20:28; The New Testament in Modern Speech, wanda R. F. Weymouth ya wallafa) Marubuta Helenawa sukan yi amfani da wannan kalmar idan suna nufin kudin da aka biya don a fanshi mutumin da aka kama a lokacin yaki.