Mene ne Ake Nufi da ‘Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka’?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Dokar “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka” ya bayyanu a wurare dabam-dabam cikin Littafi Mai Tsarki. (Fitowa 20:12; Kubawar Shari’a 5:16; Matta 15:4; Afisawa 6:2, 3) Ya kunshi muhimman matakai hudu.
Ka nuna masu godiya. Idan ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka hakan zai nuna cewa kana godiya ga dukan abubuwan da suka yi maka. Za ka iya nuna godiyarka ta wurin bin ja-gorancinsu. (Misalai 7:1, 2; 23:26) Littafi Mai Tsarki ya karfafa ka ka yi “fahariya” da iyayenka, wato ka nuna cewa kana ji da su.—Misalai 17:6.
Ka bi dokarsu. Idan ka girmama iyayenka musamman sa’ad da kake yaro, hakan zai nuna cewa kana girmama matsayin da Allah ya ba su. Littafin Kolosiyawa 3:20 ya ce: Matasa ku “yi biyayya da iyayenku cikin kowane abu, gama wannan abin yarda ne cikin Ubangiji.” Yesu ma ya yi wa iyayensa biyayya sa’ad da yake yaro.—Luka 2:51.
Ka yi masu biyayya. (Leviticus 19:3; Ibraniyawa 12:9) Hakan ya kunshi halinka yayin da kake sadawa da su. Ko da yake a gaskiya a wasu lokuta wasu iyaye suna yin abubuwan yake yi wa yaransu wuya su yi biyayya. Duk da haka, yara za su iya girmama iyayensu ta wurin gujewa yin furuci ko kuma ayyukan da ba su dace ba. (Misalai 30:17) Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa babban laifi ne yaro ya rena mahaifinsa ko kuma mahaifiyarsa har ma wurin furucinsa.—Matta 15:4.
Ka yi masu tanadi. Iyayenka za su bukaci taimako daga wurinka yayin da suka tsufa. Za ka iya girmama su ta wurin yin iya kokarinka ka biya masu bukata. (1 Timotawus 5:4, 8) Alal misali, sa’ad da Yesu yake gab da mutuwa, ya shirya yadda za a lura da mahaifiyarsa.—Yohanna 19:25-27.
Ra’ayoyi da ba daidai ba game da girmama mahaifinka da mahaifiyarka
Ra’ayi da ba daidai ba: Girmama mahaifinka da mahaifiyarka yana nufin cewa tilas ne iyayenka su rika sa baki a aurenku.
Gaskiyar al’amarin: Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa dangantakar da ke tsakanin ma’aurata ta fi duk wata dangantaka da mutum yake da shi da danginsa. Littafin Farawa 2:24 ya ce: “Domin wannan mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa: za su zama nama ɗaya kuma.” (Matta 19:4,5) Babu shakka, ma’aurata za su iya amfana daga shawarwarin iyayensu da kuma surukansu. (Misalai 23:22) Hakazalika, ma’aurata za su iya tsai da shawara game da iyakan yadda za su rika hulda da danginsu.—Matta 19:6.
Ra’ayi da ba daidai ba: Dole ne ka bi duk dokar da iyayenka suka kafa.
Gaskiyar al’amarin: Ko da yake iyaye ne Allah ya ba iko a iyali, duk wani iko da ‘yan Adam suke da shi yana da iyaka. Me ya sa? Domin ba zai taba fin ikon da Allah yake da shi ba. Alal misali, lokacin da wani babban kotu ya umurci al’majiran Yesu cewa su yi wa Allah rashin biyayya, sun ce: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah” fiye da mutane. (Ayyukan Manzanni 5:27-29) Hakan nan ma, yara suna biyayya ga iyayensu a “cikin Ubangiji,” wato a cikin duk abin da bai saba wa dokokin Allah ba.—Afisawa 6:1.
Ra’ayi da ba daidai ba: Girmama mahaifinka da mahaifiyarka yana nufin cewa dole ne ka bi addininsu.
Gaskiyar al’amarin: Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu rika bincika ko abin da muke koya gaskiya ne. (Ayyukan 17:11; 1 Yohanna 4:1) Wanda ya yi hakan zai iya zaban bangaskiyar da ta bambanta da na iyayensa. Littafi Mai Tsarki ya ambata sunayen amintattun bayin Allah da suka ki bin addinin iyayensu, kamar su Ibrahim da Ruth da kuma manzo Bulus.—Joshua 24:2, 14, 15; Ruth 1:15, 16; Galatiyawa 1:14-16, 22-24.
Ra’ayi da ba daidai ba: Don ka nuna cewa kana girmama mahaifinka da mahaifiyarka, tilas ne ka bi al’adunsu na bauta wa kakanni.
Gaskiyar al’amarin: Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi ma Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai ma za ka bauta masa.” (Luka 4:8) Duk wanda yake bauta wa kakanninsa yana bata wa Allah rai. Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa “matattu ba su san kome ba.” Ba su san ko ana girmama su ba; balle su taimaka ko yi wa masu rai lahani.—Mai Wa’azi 9:5, 10; Ishaya 8:19.