Kudi Shi Ne Tushen Dukan Mugunta Kuwa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A’a. Littafi Mai Tsarki bai ce kudi mugun abu ba ne, kuma bai ce kudi ne ke jawo munana ayyuka ba. Furucin nan “kudi shi ne tushen mugunta” ba ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar ba ne. Abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar shi ne cewa: “Kaunar kudi ita ce tushen kowace irin mugunta.” a—1 Timoti 6:10.
Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?
Littafi Mai Tsarki ya amince cewa kudi yana da amfani. Idan ana yin amfani da kudi a hanyar da ta dace yana ma iya “tsare mutum.” (Mai-Wa’azi 7:12) Bugu da kari, Littafi Mai Tsarki ya yaba wa masu taimaka wa wasu, har da bayar da kyautar kudi.—Karin Magana 11:25.
Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi cewa kada mu sa kudi ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Ya ce: “Ku yi nesa da halin son kudi, ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi.” (Ibraniyawa 13:5) Darasin shi ne mu rika yin amfani da kudi yadda ya dace kuma mu guji neman arziki ruwa-a-jallo. A maimakon haka, mu gamsu da abin da muke da shi wato abinci da sutura da kuma wurin kwana.—1 Timoti 6:8.
Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi game da son kudi?
Masu hadama ba za su sami rai na har abada. (Afisawa 5:5) Domin hadama kamar bauta wa gumaka ne ko bauta ta karya. (Kolosiyawa 3:5) Wani dalili kuma shi ne, masu hadama sukan ki bin ka’idodi masu kyau don su sami abin da suke sha’awa. Littafin Karin Magana 28:20 ya ce: “Mai neman samun arziki da sauri, ba zai kubuta daga hukunci ba.” Za su iya fada cikin jarraba na aikata laifuffuka kamar kwace, zamba, shari, sace mutum don fansa da kuma kisan kai.
Ko da son kudi bai sa mu kasance da halaye marasa kyau ba, yana iya jawo munanan sakamako. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amma wadanda suke marmarin yin arziki sukan fādi cikin jarraba, cikin tarko na mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na banza.”—1 Timoti 6:9.
Ta yaya za mu amfana daga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kudi?
Idan muka ci gaba da yin abubuwan da Allah yake so kuma muka bi ka’idodinsa, hakan zai sa a rika daraja mu kuma Allah zai yi mana albarka da kuma goyi bayanmu. Allah ya yi wa wadanda suka faranta masa rai alkawari cewa: “Har abada ba zan bar ka ba, sam-sam ba zan yar da kai ba.” (Ibraniyawa 13:5, 6) Ban da haka, ya tabbatar mana cewa “mai aminci zai cika da albarku.”—Karin Magana 28:20.
a Ana iya fassara wannan ayar haka: “Son kudi shi ne tushen mugayen ayyuka.”