Waye ko Kuma Mene ne Kalmar Allah?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Furucin nan “maganar Allah” ko Kalmar Allah yana nufin sako daga Allah ko kuma littafin da ke dauke da wannan sakon. (Luka 11:28) A wasu wurare kuma an yi amfani da furucin nan “Kalmar Allah” ko “Kalman” a matsayin lakabi.—Ru’ya ta Yohanna 19:13; Yohanna 1:14.
Sako daga Allah. Sau da yawa annabawa sun ambata cewa sakonsu daga Allah ne. Alal misali, annabi Irmiya ya soma rubutunsa da furucin nan “maganar Ubangiji dai ta zo gareni.” (Irmiya 1:4, 11, 13; 2:1) Kafin annabi Sama’ila ya gaya wa Saul cewa Allah ya zabe shi ya zama sarki, ya ce: “Kai ka tsaya yanzu domin in jiyar maka da maganar Allah.”—1 Sama’ila 9:27.
A matsayin lakabi. An yi amfani da wannan furuci “Kalman” a cikin Littafi Mai Tsarki a matsayin lakabi sa’ad da ake magana game da Yesu Kristi a lokacin da yake sama da kuma lokacin da ya yi hidima a duniya. Ka yi la’akari da dalilan da suka sa muka amince da hakan:
An halicci Kalman kafin sauran abubuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin farko akwai Kalma, . . . Wannan a cikin farko tare da Allah yake.” (Yohanna 1:1, 2) Yesu “dan fari ne gaban dukan halitta . . . shi ne kuwa gaba da dukan abu.”—Kolosiyawa 1:13-15, 17.
Kalman ya zo duniya a matsayin mutum. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kalman ya zama jiki, ya zauna a wurinmu.” (Yohanna 1:14) Yesu Kristi ya “wofinta kansa da ya dauki surar bawa, yana kasancewa da sifar mutane.”—Filibbiyawa 2:5-7.
Kalman Dan Allah ne. Bayan manzo Yohanna ya ce “Kalman ya zama jiki,” kamar yadda muka ambata a baya, ya ƙara cewa: “Muka duba daukakarsa, kamar ta haifaffe kadai daga wurin Uba.” (Yohanna 1:14) Ban da haka ma, Yohanna ya ce: “Yesu Dan Allah ne.”—1 Yohanna 4:15.
Kalman yana da halaye irin na Allah. “Kalman kuwa Allah ne.” (Yohanna 1:1) Yesu shi ne “hasken daukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma.”—Ibraniyawa 1:2, 3, Littafi Mai Tsarki.
Kalman yana sarauta. Littafi Mai Tsarki ya ce akwai “kambin sarauta masu-yawa” a kan Kalman Allah. (Ru’ya ta Yohanna 19:12, 13) An kuma kira Kalman “Sarkin Sarakuna, da Ubangijin iyayengiji.” (Ru’ya ta Yohanna 19:16) Ban da haka ma, an kira Yesu “Sarkin sarakuna da Ubangijin wadanda suke sarauta.”—1 Timotawus 6:14, 15, New World Translation.
Kalman yana magana a madadin Allah ne. Lakabin nan “Kalman” yana nufin wanda Allah yake amfani da shi don ya idar da sako ko umurni. Yesu ya ce ya yi hakan. Ya ce: “Uba wanda ya aiko ni, shi ne ya ba ni umurni, abin da zan fadi, da magana da zan yi kuma. . . . Kamar yadda Uba ya fada mini, haka ni ke magana.”—Yohanna 12:49, 50.