Mene Ne Mulkin Allah?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Mulkin Allah gwamnati ce ta ainihi da Jehobah Allah ya kafa. A cikin Littafi Mai Tsarki ana ce da “mulkin Allah,” “mulkin sama” domin yana sarauta daga sama. (Markus 1:14, 15; Matta 4:17) Gwamnati ce irin ta mutane, duk da haka ta fi ta mutane a kowane fasali.
Masarauta. Allah ya naɗa Yesu Kristi Sarkin Mulkin kuma ya ba shi iko fiye da wani masarauci ɗan Adam da ake da shi. (Matta 28:18) Yesu yana amfani da wannan ikon a yin nagarta ne kawai, tun da yake ya nuna cewa shi Shugaba ne wanda za a iya dogara gareshi kuma mai juyayi. (Matta 4:23; Markus 1:40, 41; 6:31-34; Luka 7:11-17) Tare da jagorar Allah, Yesu ya zaɓi mutane daga dukan al’ummai da za su yi “mulki bisa duniya” da shi a sama.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.
Tsawon Lokacin. Mulkin Allah za ya “tsaya har abada,” ba kamar gwamnatoci na ’yan Adam da yau suna nan goɓe ba su ba.—Daniel 2:44.
Talakawan. Duk wanda ya yi abin da Allah ke bukata gareshi zai iya zama talikin Mulkin Allah, ko daga ina ya fito.—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.
Dokoki. Dokoki (ko kuwa umurnan) Mulkin Allah ba haramta munanan halaye ne kawai za su yi ba. Suna tsabtata ɗabi’ar talakawan. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka kuma ita ce ta fari. Ta biyu mai-kamaninta kuma ta ce, “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:37-39) Ƙaunar Allah da maƙwabci zai sa talakawan Mulkin su aikata da kyau yadda zai amfane wasu.
Ilimi. Da yake Mulkin Allah zai kafa wa talakawansa mizanai, zai kuma koyar da mutane yadda za su bi mizanan.—Ishaya 48:17, 18.
Aikin. Mulkin Allah ba zai wadata masu sarautan kuma ya cuci talakawansa ba. Maimakon haka, zai cika nufin Allah, har da alkawarinsa cewa waɗanda suke ƙaunarsa za su rayu har abada a duniya.—Ishaya 35:1, 5, 6; Matta 6:10; Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.