Wane Zunubi Ne Adamu da Hauwa’u Suka Yi?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Adamu da Hauwa’u ne mutanen da suka fara yin zunubi. A lokacin da suka yi ma Allah rashin biyayya kuma suka ci daga ‘itacen sanin nagarta da mugunta,’ sun yi zunubi na farko. (Farawa 2:16, 17; Romawa 5:19) Ba a yarda Adamu da Hauwa’u su ci daga itacen nan ba domin itacen yana wakiltar ikon Allah da hakkinsa na yanke shawara a kan abin da ya dace da wanda bai dace ba. Da suka ci daga wannan itacen, Adamu da Hauwa’u sun nuna cewa sun fi so su da kansu su zabi abin da ya dace da wanda bai dace ba. Ta yin hakan sun nuna cewa sun ki sarautar Allah.
Ta yaya zunubi ya shafi Adamu da Hauwa’u?
Bayan zunubin da suka yi, Adamu da Hauwa’u sun tsufa har a karshe suka mutu. Sun bata dangantakarsu da Allah kuma sun rasa begen rayuwa ta har abada a cikin koshin lafiya.—Farawa 3:19.
Ta yaya zunubin Adamu da Hauwa’u ya shafe mu?
Kamar yadda yara suke gādan wasu cututtuka daga iyayensu, yaran Adamu da Hauwa’u sun gāji zunubi daga wurinsu. (Romawa 5:12) Hakan ya sa an haifi dukan mutane a “cikin zunubi.” a Ma’ana, mu ajizai ne kuma yana da sauki mu yi abin da bai dace ba.—Zabura 51:5, Tsohuwar Hausa a Saukake; Afisawa 2:3.
Domin zunubin da muka gāda, dukanmu muna fama da ciwo da tsufa da mutuwa. (Romawa 6:23) Muna kuma fama da sakamakon kurakuranmu da na wasu.—Mai wa’azi 8:9; Yakub 3:2.
Za mu iya samun ’yanci daga zunubin da Adamu da Hauwa’u suka yi?
Kwarai kuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya ba da ransa “domin ya zama hadaya ta daukar alhakin zunubanmu.” (1 Yohanna 4:10) Hadayar da Yesu ya ba da za ta sa mu sami ’yanci daga zunubin da muka gāda, kuma za ta sa mu sami abin da Adamu da Hauwa’u suka rasa, wato rai na har abada a cikin koshin lafiya.—Yohanna 3:16. b
Koyarwar karya game da zunubin da Adamu da Hauwa’u suka yi?
Karya: Domin mu masu zunubi ne, ba za mu taba iya kulla dangantaka mai kyau da Allah ba.
Gaskiya: Allah ba ya dora mana laifi don zunubin Adamu da Hauwa’u. Ya san cewa mu ajizai ne, kuma ba ya bukatar mu yi abin da ya fi karfinmu. (Zabura 103:14) Ko da yake mu masu zunubi ne, za mu iya kulla dangantaka mai kyau da Allah.—Karin Magana 3:32.
Karya: Yin baftisma yana sa mu sami ’yanci daga zunubi, saboda haka, jarirai ma suna bukatar yin baftisma.
Gaskiya: Ko da yake baftisma tana da amfani don samun ceto, ba da gaskiya ga hadayar Yesu ne kadai za ta iya share zunubin mutum. (1 Bitrus 3:21; 1 Yohanna 1:7) Bangaskiya ta dangana ne ga abubuwan da mutum ya koya daga Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, jarirai ba za su iya kasancewa da bangaskiya ba. Don haka, Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan yi wa jarirai baftisma ba. Kiristoci a karni na farko ma ba su yi hakan ba. “Maza da mata” da suka ba da gaskiya ga Kalmar Allah ne suka yi wa baftisma ba jarirai ba.—Ayyukan Manzanni 2:41; 8:12.
Karya: Allah ya la’anci mata saboda Hauwa’u ce ta fara cin ’ya’yan itacen.
Gaskiya: Allah bai la’anci mata ba, amma ya la’anci wanda ya yaudari Hauwa’u ta yi zunubi, wato “macijin nan na tun dā, wanda ake ce da shi Mugun, ko kuma Shaidan.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9; Farawa 3:14) Kari ga haka, Adamu ne Allah ya ba wa laifin yin zunubi, ba matarsa ba.—Romawa 5:12.
Me ya sa Allah ya ce Adamu zai yi mulki a kan matarsa? (Farawa 3:16) A lokacin da Allah ya yi wannan furucin, ba wai yana nuna cewa ya amince da wannan halin ba ne, amma yana fadan sakamako da zunubin zai jawo. Allah yana so maza su kaunaci matansu kuma su daraja dukan mata.—Afisawa 5:25; 1 Bitrus 3:7.
Karya: Jima’i ne ainihin zunubin da Adamu da Hauwa’u suka yi.
Gaskiya: Ainihin zunubin da Adamu da Hauwa’u suka yi ba jima’i ba ne. Ga abin da ya sa muka fadi hakan:
Allah ya umurci Adamu kada ya ci daga itacen sanin nagarta da mugunta a lokacin da yake shi kadai, babu mata.—Farawa 2:17, 18.
Allah ya umurci Adamu da Hauwa’u cewa: “Ku yi ta haihuwa sosai ku yalwata,” wato su haifi ’ya’ya. (Farawa 1:28) Zalunci ne idan Allah ya hukunta Adamu da Hauwa’u domin sun yi abin da ya umurce su su yi.
Adamu da Hauwa’u ba su yi zunubi a lokaci daya ba, Hauwa’u ce ta fara yi, sa’an nan Adamu.—Farawa 3:6.
Allah ya amince da jima’i tsakanin miji da matarsa.—Karin Magana 5:18, 19; 1 Korintiyawa 7:3.
a A Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “zunubi” ta kunshi ajizanci da kuma yanayin da muka gāda daga iyayenmu, ba aikata laifuffuka kadai ba.
b Don samun karin bayani game da hadayar Yesu da kuma yadda za ta amfane mu, ka duba talifin nan “Ta Yaya Yesu Ya Cece Mu?”