30 GA JANAIRU, 2017
KOLOMBIYA
Kungiyar Fassara Yaren Kurame na Kasar Colombia Ta Ba Shaidun Jehobah Lambar Yabo
BOGOTA, Colombia—National Association of Sign-Language Translators/Interpreters da kuma Interpreter Guides of Colombia ANISCOL (Kungiyar fassarar yaren kurame da kuma tafinta da masu bayyana tsarin fassara ta kasar Colombia) tare da kungiyoyi daga yankuna biyu, sun ba Shaidun Jehobah lambar yabo a lokacin taronsu na kasa baki daya da aka yi a ranar 7-9 ga Octoba, 2016. Wannan shi ne taro na farko da aka shirya saboda mafassara da masu bayyana tsarin fassara, don wadanda suka ba da kansu domin su taimaka wa kurame da makafi a Colombia.
An gayyaci Shaidun Jehobah zuwa taron domin a ba su lambar yabo da ya nuna cewa an amince da “gagarumin aikin da suke yi na wallafa littattafan addini da kuma ayyuka masu kyau da suke wa kuramen kasar Colombia.” Ricardo Valencia Lopez daya daga cikin wadanda suka tsara shirin Association of Interpreters, Interpreter Guides, and Translators of Colombian Sign Language in the Coffee Axis, ASINTEC (wato Kungiyar Mafassara da Masu bayyana tsarin fassara da Mafassaran yaren kurame na Colombia) da kuma shugaban, sun bayana cewa an gayyaci Shaidun Jehobah ne domin “sun taimaka wajen bunkasa aikin fassarar yaren kurame sosai ta wurin buga ingantaccen littafi wanda ake amfani da shi sosai yayin da ake yin fassarar yaren.”
A lokacin da ake taron, Shaidun Jehobah sun yi wani gabatarwa da ya nuna abubuwan da suke yi a aikinsu na fassara da kuma tafinta. Mutanen sun ji dadin jin wadannan abubuwan, kuma hakan ya sa kwamitin da suka shirya wannan taron suka kuma kara masu wata lambar yabo domin irin kalaman da jama’a suka yi saboda abin da Shaidun suka yi a wurin taron.
Cristian Davis Valencia, wani mai sana’ar zane-zane daga Pereira da ya halarci taron ya ce ya yi “mamakin ganin cewa wani addini ya shirya wani tsarin illimantarwa mai kyau haka,” musamman ma don ba a biyan Shaidun su yi wannan aikin.
Wilson Torres, kakakin Shaidun Jehobah na Colombia, ya ce: “Tun shekara ta 2000 ne muke tanadar da littattafan da za su taimaka wa kurame. A dandalinmu a yanzu muna da bidiyoyi fiye da 400 da aka yi domin manya da matasa da yara wadanda suke yin yaren kurame na Colombia. Za mu ci gaba da tanadar da Littattafan da Ke Bayyana Littafi Mai Tsarki kyauta, kamar yadda muke yi da duk littattafan da mu ke bugawa.”
Mafassara na Shaidun Jehobah a fadin duniya suna shirya da kuma rarraba bidiyoyi dabam-dabam cikin yaren kurame 88. Shaidun Jehobah sun kuma fitar da manhajar JW Library Sign Language app da zai taimaka ma wadanda suke so za su saukar da kuma iya kallon bidiyo na yaren kurame daga dandalinmu na jw.org a saukake.
Inda Aka Samo Labarin:
International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000
Colombia: Wilson Torres, +57-1-8911530