Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Anatoliy Tokarev tare da matarsa, Margarita, da dansu, Andrey, da kuma ’yarsu, Yekaterina

8 GA OKTOBA, 2020
RASHA

Ana So A Yanke wa Dan’uwa Anatoliy Tokarev Hukuncin Yin Shekara Uku da Rabi a Kurkuku a Rasha

Ana So A Yanke wa Dan’uwa Anatoliy Tokarev Hukuncin Yin Shekara Uku da Rabi a Kurkuku a Rasha

Ranar da Za A Yanke Hukuncin

A ranar 23 ga Oktoba, 2020, * Kotun Gundumar Oktyabrsky da ke birnin Kirov zai sanar da hukuncinsa a kan Dan’uwa Anatoliy Tokarev. Mai yiwuwa a kai shi kurkuku na tsawon shekara uku da rabi.

Karin Bayani

Anatoliy Tokarev

  • Shekarar Haihuwa: 1958 (Baranovskaya, Yankin Kirov)

  • Tarihi: Mahaifiyar shi ce ta yi renon shi. Ya yi aiki a matsayin injiniya mai kirkiro manhajar kwamfuta, amma yanzu ya yi ritaya. Yana son daukan hoto, kuma yana jin dadin buga wasan darar chess da abin kida ta zamani da ake kira, accordion. Ya auri Margarita a 1979, kuma suna da yara biyu

  • Bayan ya zama dan kimiyya ne ya yi imani cewa ba Allah. Da ya kai shekara 27, sai ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, kuma a lokacin ne ya gano cewa abin da Kiristoci suka yi imani da shi, bai saba wa koyarwar kimiyya ba

Yadda Labarin Ya Soma

A ranar 24 ga Mayu, 2019, jami’an tsaro daga Russia’s Center for Countering Extremism sun kai farmaki gidan da Dan’uwa Tokarev yake. Sai jami’an tsaron suka soma tuhumar Dan’uwa Tokarev. Sun ce za su kai iyalin Dan’uwa Tokarev kotu idan bai amince cewa ya yi ayyukan tsattsauran ra’ayin ba. Daga nan, aka dauki Dan’uwa Tokarev zuwa wani ofishin da ake yi wa mutane tambayoyi.

Kusan watanni biyar bayan haka, an zargi Dan’uwa Tokarev da aikata laifi a karkashin kudin dokoki na Criminal Code of the Russian Federation. An zarge shi da ba da tallafin kudi ga kungiyar ’yan tsattsauran ra’ayi. Mai shigar da karar yana amfani da maganar da suka dauka a na’ura a boye a gidan Dan’uwa Tokarev. Ta wannan na’urar, mai shigar da karar yana da’awar cewa Dan’uwa Tokarev yana shirya taro, inda ake amfani da haramtattun littattafai masu dauke da tsattsauran ra’ayi.

Muna addu’a a madadin Dan’uwa Tokarev da iyalinsa, kuma mun tabbata cewa Jehobah zai ci gaba da nuna musu “aminci.”​—⁠Zabura 18:​25, Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 3 Za a iya canja ranar