Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa Yevgeniy Spirin da matarsa, Natalya

14 GA OKTOBA, 2020
RASHA

Kotun Daukaka Kara a Rasha Ya Goyi Bayan Hukuncin da Aka Yanke wa Dan’uwa Spirin Cewa Zai Biya Tara

Kotun Daukaka Kara a Rasha Ya Goyi Bayan Hukuncin da Aka Yanke wa Dan’uwa Spirin Cewa Zai Biya Tara

A ranar 14 ga Oktoba, 2020, Kotun Yankin Ivanovo ya hukunta cewa laifin da aka kama Dan’uwa Yevgeniy Spirin da shi da tarar da aka ci masa a watan Yuli 2020 ya dace. Wadanda suka shigar da karar sun so a sake saurarar karar amma kotun daukaka karar ya ki amincewa da hakan. Da alama wadanda suka shigar da karar za su sake daukaka kara, domin tun farko, abin da suke so shi ne a kai dan’uwan kurkuku na tsawon shekara bakwai.