Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

27 ga Janairu–2 ga Fabrairu

ZABURA 140-143

27 ga Janairu–2 ga Fabrairu

Waƙa ta 44 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ka Riƙa Yin Abubuwan da Suka Jitu da Adduꞌoꞌinka

(minti 10)

Ka riƙa karɓan shawara (Za 141:5; w22.02 12 sakin layi na 13-14)

Ka yi tunani a kan yadda Jehobah yake taimaka mana da yadda ya taimaka wa bayinsa a dā (Za 143:5; w10 3/15 32 sakin layi na 4)

Mu yi ƙoƙari mu zama da raꞌayin Jehobah (Za 143:10; w15 3/15 32 sakin layi na 2)

Zabura 140-143 na ɗauke da adduꞌar da Dauda ya yi don neman taimako. Ban da haka ma, surorin na ɗauke da furuci da suka nuna cewa ya yi abubuwan da suka jitu da adduꞌar da ya yi.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 140:3—Me ya sa Dauda ya kwatanta harshen mugaye da macizai masu zafin dafi? (it-2-E 1151)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 141:​1-10 (th darasi na 12)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Bayan ka taimaka ma wani da yake bukatar taimako, ka yi masa waꞌazi. (lmd darasi na 3 batu na 5)

5. Komawa Ziyara

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Mutumin ya gaya maka cewa ya shaƙu da ayyuka. (lmd darasi na 7 batu na 3)

6. Ka Bayyana Imaninka

(minti 5) Gwaji. ijwfq talifi na 21—Jigo: Me Ya Sa Ba Ku Yarda da Karin Jini? (th darasi na 7)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 141

7. Zai Dace Mu Yi Shiri Yanzu Kafin Mu Bukaci Jinya ko Tiyata

(minti 15) Tattaunawa.

Jehobah ya yi mana alkawari cewa zai zama mai taimakonmu na “kurkusa lokacin wahala.” (Za 46:1) Yin jinya ko tiyata zai iya sa mutum damuwa sosai. Duk da haka, Jehobah ya tanadar mana da duka abubuwan da muke bukata idan mun fuskanci yanayoyin nan. Alal misali, ƙungiyarmu ta yi mana tanadin takardar Izinin Kula da Jinya (DPA) da Katin Gabatarwa, a da wasu takardu da ke ɗauke da bayanai game da lafiyarmu b da kuma Kwamitin Hulɗa da Asibitoci (HLC). Tanadin nan suna taimaka mana mu yi biyayya ga umurnin Allah game da jini.—A. M 15:​28, 29

Ku kalli BIDIYON Shin Kuna a Shirye don Jinyar Gaggawa? Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya wasu ꞌyanꞌuwa suka amfana don sun cika katin DPA?

  • Ta yaya wasu suka amfana daga bayanin da ke takardar Information for Expectant Mothers (S-401)?

  • Me ya sa zai dace mu tuntuɓi HLC da zarar mun san cewa za a kwantar da mu a asibiti ko za a yi mana tiyata ko jinya kamar na cutar kansa, ko da muna ganin ba za mu bukaci ƙarin jinin ba?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 103 da Adduꞌa

a Masu shela da suka yi baftisma za su iya samun katin DPA daga wurin bawa mai kula da littattafai da kuma Katin Gabatarwa (ic) don ƙananan yaransu.

b Idan da bukata za ka iya tambayi dattawa su ba ku fom na Information for Expectant Mothers (S-401), da Information for Patients Requiring Surgery or Chemotherapy (S-407), da Information for Parents Whose Child Requires Medical Treatment (S-55).