DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ƙauna Marar Canjawa ta Allah Za Ta Kāre Mu Daga Ƙarairayin Shaiɗan
Shaiɗan yana so mutane su gaskata cewa Jehobah ne yake jawo munanan abubuwa (Ayu 8:4)
Zai so mu yi tunani cewa Jehobah bai damu ba ko muna riƙe da aminci ko aꞌa (Ayu 9:20-22; w15 9/1 12 sakin layi na 3)
Ƙaunar Jehobah marar canjawa tana sa mu guji ƙarairayin Shaiɗan kuma mu riƙe aminci ga Jehobah (Ayu 10:12; Za 32:7, 10; w21.11 6 sakin layi na 14)
KA GWADA WANNAN: Ka lura da hanyoyi da Jehobah yake nuna maka ƙauna marar canjawa, ka rubuta kuma ka riƙa dubawa a kai a kai. Hakan zai taimaka idan kana fama da matsaloli.