SASHE NA 1
Allah Ya Damu da Mu Kuwa?
A YAU duniya tana cike da wahaloli. Yaƙe-yaƙe, bala’o’i, cuta, talauci, rashawa, da kuma mugunta iri-iri sun addabi miliyoyin mutane. Kai ma kana iya fuskantar damuwa ta yau da kullum. Wane ne zai iya taimaka mana? Akwai wanda ya damu kuwa?
Muna da tabbaci cewa Allah ya damu da mu ƙwarai da gaske. A cikin Kalmarsa Mai Tsarki, ya ce: “Ya yiwu mace ta manta da ɗanta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin ɗan cikinta ba? i, ya yiwu waɗannan su manta, amma ni ba ni manta da ke ba.” a
Hakan yana da ban ƙarfafa, ko ba haka ba? Ƙaunar da Allah yake nunawa ta fi ta mahaifiya ga jaririnta—ɗaya daga cikin motsin rai mafi girma na ’yan Adam. Allah ba zai taɓa watsar da mu ba! Hakika, ya riga ya kawo mana ɗauki a hanya mai ban mamaki. Ta yaya? Ta wajen nuna mana abin da zai taimaka mana mu samu rayuwar da ke cike da farin ciki, wato, cikakken imani.
Kasancewa da cikakken imani zai sa ka farin ciki. Irin wannan imanin zai taimake ka ka guji matsaloli da yawa kuma ka yi nasara wajen bi da matsalolin da ba za ka iya guje wa ba. Zai kuma jawo ka kusa da Allah, kuma ka samu kwanciyar hankali da zuciya. Cikakken imani zai sa ka samu wani abu mai ban al’ajabi a nan gaba, wato, rai na har abada a Aljanna!
Amma menene cikakken imani? Kuma ta yaya za ka iya gina shi?
a Duba Ishaya 49:15 a cikin Nassosi Masu Tsarki.