Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA

Ya Kāre Bauta ta Gaskiya

Ya Kāre Bauta ta Gaskiya

1, 2. (a) A wace hanya ce mutanen Iliya suke shan wahala? (b) Wace hamayya ce Iliya ya fuskanta a Dutsen Karmel?

ILIYA ya kalli jama’a da suke hawan Dutsen Karmel. Har wayewar gari, za ka ga cewa waɗannan mutanen suna fama da talauci da kuma yunwa. Fari na shekara uku da rabi ya ci jikinsu sosai.

2 A cikin jama’ar akwai annabawan Baal 450 masu fahariya da kuma baƙar ƙiyayya ga Iliya, annabin Jehobah. Sarauniya Jezebel ta kashe bayin Jehobah da yawa, amma wannan mutumin ya yi tsayin daka wajen yin gāba da bautar Baal. Amma har yaushe zai ci gaba da yin hakan? Wataƙila waɗannan firistoci suna ganin shi kaɗai ba zai iya cin nasara a kan dukansu ba. (1 Sar. 18:4, 19, 20) Sarki Ahab ma ya zo a kan karusarsa ta sarauta. Shi ma ya ƙi jinin Iliya.

3, 4. (a) Me ya sa wataƙila Iliya ya ji tsoro sa’ad da ranar take kusatowa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Wani abu mai muhimmanci zai faru a rayuwar Iliya a wannan ranar. Yayin da yake kallon mutanen da ke hawan dutsen Karmel, ya san cewa ba da daɗewa ba za su san wanda ya fi iko. Yaya ya ji sa’ad da ranar take kusatowa? Ba mutum ba ne marar tsoro, tun da yake yana “da tabi’a kamar tamu.” (Karanta Yaƙub 5:17.) Mun san cewa Iliya yana ganin ba wanda yake tare da shi da yake mutane marasa bangaskiya da sarkinsu da ya yi ridda, da kuma firistocinsu masu kisa sun kewaye shi.—1 Sar. 18:22.

4 Me kuma ya jefa Isra’ila cikin wannan matsalar? Kuma me za ka iya koya daga wannan labarin? Ka yi la’akari da bangaskiyar Iliya da yadda za mu amfana a yau.

Ƙarshen Gwagwarmaya da Aka Daɗe Ana Yi

5, 6. (a) Wane yanayi ne Isra’ilawa suke ciki? (b) Ta yaya Sarki Ahab ya ɓata wa Jehobah rai sosai?

5 A rayuwar Iliya, ya ga yadda aka yi watsi da bautar Jehobah wadda ita ce aba mafi muhimmanci, kuma bai iya canja yanayin ba. Isra’ila ta daɗe tana ƙoƙari ta yi zaɓi tsakanin bauta ta gaskiya da ta ƙarya, tsakanin bautar Jehobah Allah da bautar gumaka na al’umman da suka kewaye su. Wannan gwagwarmaya ta ƙara muni a zamanin Iliya.

6 Sarki Ahab ya ɓata wa Jehobah rai sosai sa’ad da ya auri Jezebel ’yar sarkin Sidon. Jezebel ta kuɗura niyyar yaɗa bautar Baal a ƙasar Isra’ila kuma ta kawar da bautar Jehobah. Ba tare da ɓata lokaci ba ta rinjayi Ahab. Ya gina haikali da kuma bagadi ga Baal kuma ya zama kan gaba wajen bauta wa wannan allan arna.—1 Sar. 16:30-33.

7. (a) Me ya sa bautar Baal ta zama abin ƙyama? (b) Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa babu saɓani game da tsawon fari na zamanin Iliya da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki? (Ka haɗa da akwatin.)

7 Me ya sa bautar Baal ta zama abin ƙyama? Domin ta sa mutane da yawa su daina bauta wa Allah na gaskiya. Addini ne da ake yawan lalata da mugunta. Ya ƙunshi yin karuwanci a haikali na maza da mata da rukunin mutane masu lalata da kuma yin hadaya da yara. Saboda haka, Jehobah ya aiki Iliya wurin Ahab ya gaya masa cewa za a yi fari har sai annabin Allah ya sanar da ƙarshensa. (1 Sar. 17:1) An yi shekaru kafin Iliya ya je wurin Ahab ya gaya masa ya tara mutane da kuma annabawan Baal a kan Dutsen Karmel. *

A yau ana yin yawancin abubuwan da ake yi a bautar Baal a dā

8. Mene ne za mu iya koya daga wannan labari game da bautar Baal?

8 Mene ne za mu iya koya daga wannan gwagwarmaya a yau? Wasu za su iya ji kamar wannan labari game da bautar Baal ba shi da amfani kuma, da yake ba ma ganin haikali da bagadai na Baal a yau. Amma bai kamata mu ɗauka cewa wannan labari ne kawai na zamanin dā ba. (Rom. 15:4) Kalmar nan “Baal” tana nufin mai shi ko “mai gida.” Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa su zaɓe shi a matsayin “baal” ɗin su, ko kuma maigidansu. (Isha. 54:5) Ka yarda cewa har ila mutane suna bauta wa wasu alloli da ba Allah Makaɗaici ba ne? Hakika, mutane suna mai da kuɗi da aiki da nishaɗi da jima’i ko kuma wasu alloli masu yawa mai gidansu ta wajen biɗarsu da dukan rayuwarsu maimakon bauta wa Jehobah. (Mat. 6:24; karanta Romawa 6:16.) Mutane a yau suna yin yawancin abubuwa da ake yi a bautar Baal a dā. Yin tunani a kan wannan gwagwarmaya tsakanin Jehobah da Baal za ta iya taimaka mana mu zaɓa wanda za mu bauta masa.

Ta Yaya Suke “Ɗingishi?”

9. (a) Me ya sa Dutsen Karmel ya dace don fallasa bautar Baal? (Duba hasiya.) (b) Mene ne Iliya ya gaya wa mutanen?

9 Idan aka hau tsololon Dutsen Karmel, za a iya hangan biranen da ke nesa. Za a iya ganin kwarin Kishon da ke ƙasa zuwa Bahar Rum da ke kusa har zuwa duwatsun Lebanon da suke can arewa. * Sa’ad da rana ta haskaka a wannan ranar gwagwarmaya, an ga yadda farin ya busar da ko’ina. Ƙasa mai ni’ima da Jehobah ya ba ’ya’yan Ibrahim ta zama matacciya. Yanzu ƙasa ce kawai da rana take ƙonawa, kuma mutanen Allah ne suka halaka ta saboda wautarsu! Sa’ad da mutanen suka taru, sai Iliya ya je kusa kuma ya ce: “Har yaushe za ku yi ɗingishi a kan wannan imani da wancan? Idan Ubangiji shi ne Allah, ku bi shi; amma idan Baal ne, sai ku bi shi.”—1 Sar. 18:21.

10. Ta yaya mutanen Iliya suke “ɗingishi a kan wannan imani da wancan,” kuma mene ne suka mance?

10 Mene ne Iliya yake nufi da furucin nan “ɗingishi a kan wannan imani da wancan?” Waɗannan mutanen ba su fahimci cewa wajibi ne su zaɓa ko za su bauta wa Jehobah ko kuma Baal ba. Suna tsammanin za su iya yin haɗin bauta, su faranta wa Baal rai ta bukukuwansu masu ban ƙyama kuma har ila su nemi tagomashin Jehobah Allah. Wataƙila sun yi tunanin cewa Baal zai albarkaci gonakinsu da tumakinsu, “Ubangiji mai-runduna” kuma zai kāre su a baƙin daga. (1 Sam. 17:45) Sun mance cewa Jehobah yana so a bauta masa shi kaɗai, kamar yadda mutane da yawa a yau ma ba su fahimta ba. Yana bukatar a bauta masa shi kaɗai kuma ya cancanci haka. Ba ya amincewa da wanda yake haɗin bauta, domin hakan yana ɓata masa rai!—Karanta Fitowa 20:5.

11. Ta yaya kake ganin furucin Iliya a Dutsen Karmel zai taimaka mana mu sake bincika abubuwan da suke da muhimmanci a gare mu da kuma bautarmu?

11 Saboda haka, waɗannan Isra’ilawa suna “ɗingishi” ko kuma sun kasa tsai da shawara kamar mutumin da yake ƙoƙari ya bi hanya biyu a lokaci ɗaya. Mutane da yawa a yau suna yin irin wannan kuskure ta wajen ƙyale wasu abubuwa su kasance da muhimmanci a rayuwarsu fiye da bautar Allah! Bin shawarar da Iliya ya ba su cewa su daina ɗingishi a kan abubuwa biyu, zai iya taimaka mana mu sake yin la’akari da bautarmu da kuma abubuwan da suka fi fifiko a rayuwarmu.

Gwaji na Ƙarshe

12, 13. (a) Wane gwaji ne Iliya ya ce a yi? (b) Ta yaya za mu nuna cewa mun dogara ga Jehobah kamar Iliya?

12 Sai Iliya ya ba da shawara cewa a yi wani gwaji mai sauƙi. Firistocin Baal za su kafa bagadi su miƙa hadaya a kai, sai kuma su yi wa allansu addu’a ya ƙona hadayar. Iliya ma zai yi hakan. Ya ce: “Allahn da ya amsa da wuta, shi za shi zama Allah” wato, Allah na gaskiya. Iliya ya san Allah na gaskiya. Ya yi imani da shi sosai, shi ya sa bai yi jinkirin ƙyale annabawan Baal su fara ba. Ya ƙyale su su zaɓi bijiminsu domin hadaya kuma su soma tuntuɓar Baal. *1 Sar. 18:24, 25.

13 Jehobah ba ya yin mu’ujiza a zamaninmu. Duk da haka, muna iya dogara ga Jehobah kamar Iliya, domin bai canja ba. Alal misali, sa’ad da wasu suka ƙi amincewa da koyarwar Littafi Mai Tsarki, kada mu ji tsoron ƙyale su su faɗi ra’ayinsu. Kamar Iliya, mu dogara ga Allah ya taimaka musu su fahimci koyarwarsa. Kada mu dogara ga kanmu, amma mu dogara ga Kalmarsa, wadda aka tsara domin “kwaɓewa.”—2 Tim. 3:16.

Iliya ya san cewa bauta wa Baal wauta ce, kuma yana son mutanen Allah su fahimci haka

14. Ta yaya Iliya ya yi wa masu bauta wa Baal ba’a, kuma me ya sa?

14 Sai annabawan Baal suka shirya hadayarsu kuma suka nemi taimakon allansu. Suka yi ta roƙo, suna cewa: “Ya Baal, ka ji mu.” Sun ci gaba da yin hakan kuma lokaci yana shigewa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amma babu murya, ba kuwa wanda ya amsa.” Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya fara yi musu ba’a, yana cewa wataƙila Baal ya duƙufa ne cikin wani aiki shi ya sa bai amsa ba, wai wataƙila ya ratse ne, ko kuma ana bukatar wani ya tashe shi daga barci. Iliya ya gaya wa waɗannan annabawan ƙarya: “Ku yi ihu.” Iliya ya san cewa bauta wa Baal wauta ce, kuma yana son mutanen Allah su fahimci haka.—1 Sar. 18:26, 27.

15. Ta yaya batun annabawan Baal ya nuna cewa wauta ce mu mai da wani abu dabam Allahnmu?

15 Sai firistocin Baal suka haukace na ɗan lokaci, “suka yi ihu, suka tsatsage jikinsu da wuƙaƙe da māsu, bisa ga adarsu, har jini ya ɓulɓulo musu.” Amma duka a banza! “Babu murya, ba kuwa wanda ya amsa, ko wanda ya kula.” (1 Sar. 18:28, 29) Hakika, baal ƙage ne kawai da Shaiɗan ya kafa domin ya rinjayi mutane su daina bauta wa Jehobah. Gaskiyar zancen ita ce, za mu jawo wa kanmu baƙin ciki da kuma kunya idan muka mai da wani abu dabam Allahnmu.—Karanta Zabura 25:3; 115:4-8.

An Amsa

16. (a) Mene ne wataƙila mutanen suka tuna sa’ad da Iliya yake gyara bagadi a Dutsen Karmel? (b) Ta yaya Iliya ya nuna cewa ya dogara ga Allahnsa?

16 Yanzu da yamma ta kusa, lokaci ne da Iliya zai miƙa nasa hadaya. Sai ya gyara bagadin Jehobah da waɗanda suke gāba da bauta ta gaskiya suka rusa. Ya yi amfani da duwatsu 12, wataƙila don ya tuna wa ƙabilu 10 na Isra’ila cewa dole ne su bi Doka da aka bai wa ƙabilu 12. Sai ya ɗora hadayarsa a kan bagadi, kuma ya sa aka jiƙa kome da ruwa da wataƙila aka ɗebo daga Bahar Rum da ke kusa. Ya sa aka tona rami kewaye da bagadin kuma aka cika shi da ruwa. Iliya ya sa annabawan Baal su shirya hadayarsu yadda wuta za ta yi saurin ƙona ta, amma bai yi hakan ba ga Jehobah, domin ya dogara ga Allahnsa.—1 Sar. 18:30-35.

Addu’ar Iliya ta nuna cewa har yanzu yana ƙaunar mutanensa, domin yana ɗokin ganin Jehobah ya sa sun canja “zukatansu”

17. Ta yaya addu’ar Iliya ta nuna abubuwan da suka fi muhimmanci a gare shi, kuma yaya za mu iya yin koyi da shi sa’ad da muke addu’a?

17 Sa’ad da aka gama shirya kome, sai Iliya ya yi addu’a mai motsawa da ta nuna abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsa. Da farko, yana so mutanen su san cewa Jehobah ne “Allah cikin Isra’ila,” ba Baal ba. Na biyu, yana so kowa ya sani cewa shi bawan Jehobah ne, kuma dukan wani yabo da ɗaukaka ga Allah ne. A ƙarshe, ya nuna cewa har yanzu yana ƙaunar mutanensa, domin yana ɗokin ganin Jehobah ya sa sun canja “zukatansu.” (1 Sar. 18:36, 37) Har ila Iliya yana ƙaunarsu, duk da wahala da suka jawo wa kansu domin rashin amincinsu. Sa’ad da muke addu’a, shin za mu nuna cewa sunan Allah ne ya fi muhimmanci a gare mu, kuma mu nuna cewa mun damu da waɗanda suke bukatar taimako?

18, 19. (a) Ta yaya Jehobah ya amsa addu’ar Iliya? (b) Mene ne Iliya ya umurci mutanen su yi, kuma me ya sa bai kamata a yi wa annabawan Baal jin ƙai ba?

18 Kafin Iliya ya yi addu’a, wataƙila wannan taron jama’a tana mamaki ko Jehobah zai kasance kamar Baal. Amma nan da nan bayan addu’ar, sai wani abin mamaki ya faru. Labarin ya ce: “Da wannan, sai wutar Ubangiji ta fāɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsu, da ƙura, ta shanye ruwan wuriya.” (1 Sar. 18:38) Hakika, wannan amsa ce ta musamman ga addu’ar Iliya! Mene ne mutanen suka yi?

“Da wannan, sai wutar Ubangiji ta fāɗo”

19 Dukansu suka ce: “Shi ne Allah; Ubangiji [Jehobah] shi ne Allah.” (1 Sar. 18:39) A ƙarshe, gaskiya ta fito ɓalo-ɓalo. Duk da haka, mutanen ba su kasance da bangaskiya ba tukuna. Me ya sa? Domin sun yarda ne kawai cewa Jehobah ne Allah na gaskiya bayan sun ga wuta ta faɗo daga sama. Saboda haka Iliya ya bukaci mutanen su nuna bangaskiyarsu ta wajen yin wani abu. Ya ce su yi abin da suka ƙi yi shekaru da suka shige, wato biyayya ga Dokar Jehobah da ta ce a kashe annabawan ƙarya da kuma masu bautar gumaka. (K. Sha 13:5-9) Waɗannan firistocin Baal abokan gaban Jehobah Allah ne kuma sun ƙi yin biyayya ga nufinsa da gangan. Sun cancanci a ji ƙansu ne? A’a, don firistocin ba su nuna jin ƙai ga yara marasa laifi da aka ƙona su da rai domin hadaya ga Baal ba. (Karanta Misalai 21:13; Irm. 19:5) Waɗannan mutane ba su cancanci a yi musu jin ƙai ba ko kaɗan. Saboda haka, Iliya ya ba da umurni a kashe su kuma aka yi hakan.—1 Sar. 18:40.

20. Me ya sa ra’ayin masu sūkar labarin Iliya bai dace ba?

20 Masu sūkar labarin Iliya a yau ba su yarda da wannan gwaji na ƙarshe da aka yi a Dutsen Karmel ba. Wasu sun damu cewa masu tsattsauran ra’ayi na addini za su yi amfani da wannan don su halalta ayyukan mugunta da sunan addini. Kuma abin baƙin ciki, mutane da yawa a yau suna yin ayyukan mugunta masu yawa da sunan addini. Duk da haka, Iliya ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne. Yana aiki ne a madadin Jehobah ta wajen yin kisa da ta dace. Bugu da ƙari, Kiristoci na gaskiya sun san cewa ba za su iya bin tafarkin Iliya ba ta wajen ɗaukan takobi su yaƙi miyagu. Maimakon haka, suna bin mizanan da Yesu ya kafa wa almajiransa sa’ad da ya ce wa Bitrus: “Mayar da takobinka gidansa: gama dukan waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi za su lalace.” (Mat. 26:52) Jehobah zai yi amfani da Ɗansa wajen zartar da hukuncinsa a nan gaba.

21. Me ya sa ya dace Kiristoci na gaskiya a yau su yi koyi da misalin Iliya?

21 Wajibi ne Kiristoci na gaskiya su kasance da bangaskiya. (Yoh. 3:16) Wani abin da zai taimaka musu shi ne yin koyi da mutane masu bangaskiya kamar Iliya. Ya bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya kuma ya aririci mutane su yi hakan. Ya fallasa addinin da Shaiɗan yake amfani da shi don ya rinjayi mutane su daina bauta wa Jehobah. Ya kuma dogara ga Jehobah ya magance matsaloli, maimakon ya dogara ga kansa da kuma iyawarsa. Hakika, Iliya ya kāre bauta ta gaskiya. Bari dukanmu mu yi koyi da bangaskiyarsa!

^ sakin layi na 9 Dutsen Karmel yana da dausayi a koyaushe, domin iska mai lema daga teku tana hurowa daga tundansa, kuma tana sa a yi ruwan sama da kuma raɓa a kai a kai. Babu shakka, wannan dutse yana da muhimmanci ga bautar Baal domin an ce shi ne yake kawo ruwan sama. Saboda haka, Karmel da ya bushe ya kasance wuri da ya dace domin fallasa yaudarar bautar Baal.

^ sakin layi na 12 Ya dace da Iliya ya gaya musu cewa: “Kada ku sa wuta a ƙarƙashin” hadayar. Wasu masana sun ce irin waɗannan masu bautar gumaka suna amfani da bagadi da ke da rami a ƙarƙashinsa saboda wuta ta fito ta bayyana kamar daga wurin Allah ne.