Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 8

Josiah Ya Yi Abokan Kirki

Josiah Ya Yi Abokan Kirki

Kana ganin yana da sauƙi mutum ya yi abin da ya dace?— Mutane da yawa suna ganin bai da sauƙi. Akwai wani yaro mai suna Josiah, kuma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa bai kasance masa da sauƙi ya yi abin da ya dace ba. Amma abokan kirki da yake da su sun taimaka masa. A yanzu za mu ƙara koya game da shi da abokansa.

Amon ne baban Josiah, kuma shi ne sarkin Yahuda. Amon mugu ne kuma ya bauta wa gumaka. Sa’ad da baban Josiah ya mutu, sai Josiah ya zama sarkin Yahuda. Amma shekarunsa takwas ne kawai! Kana ganin shi mugu ne kamar babansa?— A’a.

Zafaniya ya gaya wa mutane kada su bauta wa gumaka

Josiah yana so ya yi wa Jehobah biyayya tun yana ƙarami. Saboda haka, ya zaɓi mutanen da suke ƙaunar Jehobah ne kaɗai su zama abokansa. Kuma sun taimaki Josiah ya yi abin da ya dace. Su wane ne wasu daga cikin abokan Josiah?

Ɗaya daga cikinsu shi ne Zafaniya. Zafaniya annabi ne da ya gaya wa mutanen Yahuda cewa za su sha wahala idan suka bauta wa gumaka. Josiah ya saurari Zafaniya kuma ya bauta wa Jehobah, ba gumaka ba.

Wani abokin Josiah kuma shi ne Irmiya. Shi da Irmiya tsara ne kuma su maƙwabta ne a lokacin da suke girma. Su abokai ne sosai, shi ya sa a lokacin da Josiah ya mutu, Irmiya ya rubuta wata waƙa mai ban tausayi game da shi. Waƙar ta nuna yadda yake baƙin ciki don zai daina ganin Josiah. Irmiya da Josiah sun taimaki juna su yi abin da ya dace kuma sun yi biyayya ga Jehobah.

Josiah da Irmiya sun taimaki juna su yi abin da ya dace

Mene ne ka koya daga misalin Josiah?— Tun Josiah yana yaro, ya so ya yi abin da ya dace. Ya san cewa ya kamata ya zaɓi mutanen da suke ƙaunar Jehobah su zama abokansa. Kai ma ya kamata ka zaɓi abokai da suke ƙaunar Jehobah don su taimake ka ka yi abin da ya dace!

KARANTA NASSOSIN NAN

  • 2 Labarbaru 33:21-25; 34:1, 2; 35:25