Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 2

Yadda Rifkatu Ta Sa Jehobah Farin Ciki

Yadda Rifkatu Ta Sa Jehobah Farin Ciki

Rifkatu mace ce da take ƙaunar Jehobah. Sunan mijinta Ishaƙu. Shi ma yana ƙaunar Jehobah. Ta yaya Rifkatu da Ishaƙu suka haɗu? Mene ne ta yi da ya nuna cewa tana so ta sa Jehobah farin ciki? Bari mu koya game da Ishaƙu, mijin Rifkatu tukun.

Ibrahim da Saratu ne iyayen Ishaƙu. Suna da zama ne a ƙasar Kan’ana, kuma mutanen ƙasar ba sa bauta wa Jehobah. Amma, Ibrahim yana so ɗansa ya auri mace da take bauta wa Jehobah. Saboda haka, wataƙila bawansa Eliezer ne ya aika ya nemo wa Ishaƙu mata a wani birni mai suna Haran. Wasu dangin Ibrahim suna da zama a wannan birnin.

Rifkatu ta yarda ta yi aiki tukuru don ta debo wa rakuman ruwa

Eliezer ya yi tafiyar ne tare da wasu bayin Ibrahim. Tafiyar tana da nisa sosai, kuma sun tafi da raƙuma guda goma da ke ɗauke da abinci da tsaraba. Ta yaya Eliezer zai san macen da ya kamata ya zaɓa wa Ishaƙu? Sa’ad da Eliezer da sauran bayin suka isa birnin Haran, sai suka tsaya a bakin wata rijiya. Me ya sa? Domin Eliezer ya san cewa ba da daɗewa ba, mutane za su zo ɗibar ruwa. Sai ya yi addu’a ga Jehobah cewa: ‘Duk macen da na ce ta ba ni ruwa kuma ta yarda ta ba ni da raƙumana ruwa, to zan san cewa ita ce macen da ka zaɓa.’

Ana nan sai wata budurwa mai suna Rifkatu ta zo bakin rijiyar. Littafi Mai Tsarki ya ce ita kyakkyawa ce. Eliezer ya roƙe ta ruwa, sai ta ce: ‘Hakika, zan ba ka ruwa sa’an nan zan je in ɗiba ma raƙumanka ruwa su ma su sha.’ Ka yi tunanin yadda Rifkatu take ta ɗebo ruwa daga rijiyar domin raƙuma suna shan ruwa sosai. Ka ga yadda take aiki sosai a wannan hoton?— Eliezer ya yi mamakin yadda Jehobah ya amsa addu’arsa.

Eliezer ya ba Rifkatu abubuwa da yawa masu kyau, sai Rifkatu ta kai shi da sauran bayin gidansu. Eliezer ya gaya wa mutanenta abin da ya sa Ibrahim ya aiko shi da kuma yadda Jehobah ya amsa addu’arsa. Iyalin Rifkatu sun yi farin ciki domin Ishaƙu zai aure ta.

Rifkatu ta bi Eliezer zuwa Kan’ana kuma Ishaƙu ya aure ta

Amma kana ganin Rifkatu za ta so ta auri Ishaƙu?— Rifkatu ta san cewa Jehobah ne ya aiko Eliezer, shi ya sa a lokacin da iyalinta suka tambaye ta ko tana so ta tafi ƙasar Kan’ana don ta zama matar Ishaƙu, ta ce: ‘E, ina so in tafi.’ Ba tare da ɓata lokaci ba ta bi Eliezer. Ishaƙu ya aure ta sa’ad da aka kawo ta ƙasar Kan’ana.

Jehobah ya yi wa Rifkatu albarka domin ta yi abin da ya yake so. Daga cikin iyalinta ne aka haifi Yesu shekaru da yawa bayan zamaninta. Idan ka bi misalin Rifkatu kuma ka sa Jehobah farin ciki, Jehobah zai yi maka albarka.

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Farawa 12:4, 5; 24:1-58, 67