DARASI NA 10
Yesu Ya Yi Biyayya a Kowane Lokaci
A kowane lokaci ne yake yi maka sauƙi ka yi wa iyayenka biyayya?— A wani lokaci, yin hakan ba zai yi maka sauƙi ba. Ka san cewa Yesu ya yi wa Jehobah da kuma iyayensa biyayya?— Misalinsa zai iya taimaka maka ka yi wa iyayenka biyayya, har a lokacin da yin hakan ba zai yi maka sauƙi ba. Bari mu ƙara koya game da misalinsa.
Yesu ya zauna da Ubansa Jehobah a sama kafin ya zo duniya. Kuma a lokacin da Yesu ya zo duniya ma, ya yi iyaye. Sunayensu Yusufu da Maryamu ne. Ka san abin da ya faru kafin su zama iyayensa?—
Jehobah ya ɗauki ran Yesu daga sama kuma ya saka shi a cikin mahaifar Maryamu, domin ta haife shi. Wannan abu ne mai ban mamaki sosai! Yesu ya yi girma a cikin mahaifar Maryamu, kamar yadda jariri yake girma a cikin mamarsa. Ta haifi Yesu bayan wata tara. Da haka Maryamu da mijinta, Yusufu, suka zama iyayen Yesu.
A lokacin da Yesu ya kai ɗan shekara 12, ya yi wani abu da ya nuna cewa yana ƙaunar Ubansa Jehobah sosai. Wannan abin ya faru ne a lokacin da Yesu da iyalinsa suka yi tafiya mai nisa zuwa Urushalima don su bauta wa Jehobah. A lokacin da Maryamu da Yusufu suke komawa gida, sun nemi Yesu amma ba su gan shi ba. Ka san inda ya je?—
Mene ne Yesu yake yi a cikin haikali?
Yusufu da Maryamu suka koma Urushalima da sauri kuma suka yi ta neman Yesu. Sun damu sosai domin ba su gan shi ba. Amma bayan kwanaki uku, sai suka gan shi a cikin haikali! Ka san abin da Yesu yake yi a haikalin?— Yana koyo game da Ubansa Jehobah. Yana ƙaunar Jehobah kuma yana so ya koyi yadda zai sa Shi farin ciki. Yesu ya yi biyayya ga Jehobah a kowane lokaci, ko da yin hakan ya yi masa wuya. Ya ci gaba da yin biyayya har a lokacin da ya yi girma da kuma lokacin da yin hakan ya ƙunshi shan wahala. Yesu ya yi biyayya ga Yusufu da Maryamu kuwa?— Littafi Mai Tsarki ya ce ya yi hakan.
Mene ne ka koya daga misalin Yesu?— Ya kamata ka yi biyayya ga iyayenka, ko da yin hakan bai da sauƙi. Za ka yi hakan?—
KARANTA NASSOSIN NAN
-
Luka 1:30-35; 2:45-52
-
Afisawa 6:1
-
Ibraniyawa 5:8