Littafi Mai Tsarki—Me Ya Sa Akwai Juyi Dabam-Dabam?
Me ya sa ake da juyin Littafi Mai Tsarki da yawa a yau? Idan aka fitar da sabon juyi, kana ganin juyin zai taimaka maka ne ko zai hana ka fahimtar Littafi Mai Tsarki? Yin bincike a kan tarihin waɗannan juyin za su taimaka maka ka yi amfani da su yadda ya dace.
Amma wane ne ya rubuta ainihin Littafi Mai Tsarki kuma yaushe ya yi hakan?
AINIHIN LITTAFI MAI TSARKI
An raba Littafi Mai Tsarki zuwa kashi biyu. Kashi na ɗaya yana da littattafai guda 39 kuma yana ɗauke da “zantattukan Allah.” (Romawa 3:2) Allah ya ja-goranci wasu maza masu aminci da ruhu mai tsarki don su rubuta waɗannan littattafan. Sun yi hakan daga shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu zuwa 443, wato wajen shekaru 1,100 ke nan. Sun rubuta yawancin littattafan a Ibrananci, shi ya sa ake kiransa Nassosin Ibrananci ko kuma Tsohon Alkawari.
Kashi na biyu yana da littattafai guda 27 kuma shi ma yana ɗauke da “maganar Allah.” (1 Tasalonikawa 2:13) Allah ya ja-gorancin mabiyan Yesu Kristi su rubuta waɗannan littattafan daga shekara ta 41 bayan haihuwar Yesu zuwa 98, wato wajen shekaru 60 ke nan. Sun rubuta yawancin littattafan da Helenanci, shi ya sa ake kiransa Nassosin Helenanci ko kuma Sabon Alkawari.
Waɗannan littattafan guda 66 ne ainihin littattafan da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma saƙon da ke ciki daga Allah ne zuwa ga ’yan Adam. Amma me ya sa aka yi juyin Littafi Mai Tsarki dabam-dabam? Ga wasu dalilai uku da suka sa aka yi hakan.
-
Don mutane su iya karanta Littafi Mai Tsarki a yarensu.
-
Don a cire kuskuren da masu kofan Littafi Mai Tsarki suka yi kuma a maido da ainihin saƙon da ke cikinsa.
-
Don a canja tsofaffin kalmomin da aka daina amfani da su a yaren.
Ka yi la’akari da yadda waɗannan dalilan suka sa aka fassara wasu juyin Littafi Mai Tsarki guda biyu.
JUYIN SEPTUAGINT NA HELENANCI
Shekaru 300 kafin a haifi Yesu, wasu malaman Yahudawa sun soma fassara Nassosin Ibrananci zuwa Helenanci. Ana kiran wannan juyin Septuagint na Helenanci. Me ya sa aka fitar da wannan juyin? A lokacin, Yahudawa da yawa suna jin Helenanci fiye da Ibrananci. Don haka, wannan juyin zai taimaka musu su san “littattafai masu-tsarki.”—2 Timotawus 3:15.
Ban da haka ma, juyin Septuagint ya taimaka wa waɗanda ba Yahudawa ba su san koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ta yaya? Wani farfesa mai suna W. F. Howard ya ce: “Daga tsakiyar ƙarni na farko, yawancin Cocin Kiristoci suna amfani da wannan juyin, kuma da shi ne malamansu suke zuwa majami’u dabam-dabam don su ‘tabbatar wa mutane daga cikin nassosi cewa Yesu ne Almasihu.’ ” (Ayyukan Manzanni 17:3, 4; 20:20, Littafi Mai Tsarki) Wani mai binciken Littafi Mai Tsarki mai suna F. F. Bruce ya ce: “Wannan dalilin ne ya sa Yahudawa da yawa suka daina amfani da juyin Septuagint.”
Da almajiran Yesu suka ci gaba da rubuta sauran littattafan da ke Nassosin Helenanci, sun haɗa littattafan da juyin Septuagint na Ibrananci. Wannan ne ya zama cikakken Littafi Mai Tsarki da muke da shi a yau.
JUYIN LATIN VULGATE
Wajen shekara 300 da kammala Littafi Mai Tsarki, wani limamin addini mai suna Jerome ya fitar da juyin Littafi Mai Tsarki a yaren Latin kuma ana kiran juyin Latin Vulgate. Tun da yake da akwai juyin Latin da yawa, me ya sa ya fitar da wannan sabon juyin? Littafin nan The International Standard Bible Encyclopedia ya ce, Jerome yana so ne ya gyara “kuskuren da aka yi, ya kuma cire ƙarin bayanan da aka yi a cikin Littafi Mai Tsarki.”
Jerome ya gyara yawancin kuskuren da aka yi. Amma da shigewar lokaci, limaman coci sun kafa wata dokar da ba ta dace ba. Sun ce juyin Latin Vulgate ne kaɗai Littafi
Mai Tsarkin da za a riƙa amfani da shi, kuma an yi shekaru da yawa ana bin wannan dokar! A lokacin, mutane da yawa ba su iya yaren Latin ba. Don haka, juyin Latin Vulgate bai taimaka wa mutane su fahimci Littafi Mai Tsarki ba.AN CI GABA DA FITAR DA SABABBIN JUYI
Da shigewar lokaci, mutane sun ci gaba da fitar da sababbin juyin Littafi Mai Tsarki kamar juyin Syriac Peshitta, wanda aka wallafa a kusan ƙarni na biyar bayan haihuwar Yesu. Amma sai a ƙarni na 14 ne aka soma fassara Littafi Mai Tsarki a yaruka dabam-dabam.
A ƙarshen ƙarni na 14 ne John Wycliffe da ke Ingila ya soma fassara Littafi Mai Tsarki zuwa Turanci. Ya yi hakan don mutanen ƙasar su iya fahimtar Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, sai Johannes Gutenberg ya ƙera wata na’urar buga littattafai. Da wannan na’urar, an buga sababbin juyin Littafi Mai Tsarki kuma an rarraba su a yaruka da yawa a Turai.
Da aka ci gaba da fitar da juyi na Turanci dabam-dabam, sai wasu suka ce bai kamata a riƙa fitar da juyi dabam-dabam a yare iri ɗaya ba. Wani limamin addini a ƙarni na 18 mai suna John Lewis ya rubuta cewa: “Akwai wasu kalmomi a yaruka da aka daina amfani da su, don haka, ana bukatar a canja juyin da ke ɗauke da tsofaffin kalmomin zuwa kalmomin da mutane suke amfani da su.”
A yau, akwai abubuwa da yawa da za su taimaka wa masu binciken Littafi Mai Tsarki su gyara tsofaffin fassarar da aka yi. Suna da cikakken bayanai a kan yarukan da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kuma suna da rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā da aka samo kwana-kwanan nan. Waɗannan bayanan suna taimaka musu su san ainihin saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
Saboda haka, sababbin juyin Littafi Mai Tsarki da ake fitar da su suna da amfani sosai. Ko da yake akwai wasu juyin da muke bukatar mu yi hankali da su. Amma, idan mutanen da suke ƙaunar Allah ne suka fitar da sabon juyin Littafi Mai Tsarki, za mu amfana daga aikinsu sosai.