Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Rika Halartan Taro don Ibada?

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Rika Halartan Taro don Ibada?

“Suka lizima a cikin . . . zumunta.”​—AYYUKAN MANZANNI 2:42.

WAƘOƘI: 20, 119

1-3. (a) Ta yaya Kiristoci suka nuna cewa suna ɗokin halartan taro? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

SA’AD DA wata ‘yar’uwa mai suna Corinna take shekara 17, an kama mahaifiyarta kuma aka kai ta wani sansanin aiki mai nisa sosai. Daga baya, aka kama Corinna da kanta kuma aka kai ta wani yanki mai nisa da ake kira Saiberiya. Aka sa ta yi aiki a gona kuma aka mai da ita baiwa. Wani lokaci, ana sa ta dole ta yi aiki a waje sa’ad da ake sanyi sosai kuma ba tare da ta saka kayan sanyi ba. Duk da haka, Corinna da wata ‘yar’uwa sun yanke shawara cewa za su yi iya ƙoƙarinsu don su halarci taron ikilisiya.

2 Corinna ta ce: “Mun bar wurin aikinmu da yamma kuma muka yi tafiya zuwa wani tashan jirgin ƙasa mai nisan kilomita ashirin da biyar. Jirgin ƙasa da muka shiga ya tashi da ƙarfe biyu na dare kuma muka yi tafiyar awa shida. Muka sauka daga jirgin kuma muka yi tafiya mai nisan kilomita 10 kafin mu isa inda ake taron. Corinna ta yi farin ciki cewa ta yi wannan tafiyar. Ta ci gaba da cewa: “Mun yi nazarin Hasumiyar Tsaro kuma muka rera waƙoƙin Mulki a taron. Mun ji daɗi don taron ya ƙarfafa mu sosai.” Waɗannan ‘yan’uwa mata sun koma bakin aikinsu kwanaki uku bayan haka, amma mai gonar bai san cewa sun bar gonar ba.

3 Bayin Jehobah suna jin daɗin kasancewa tare a kowane lokaci. Alal misali, a ƙarni na farko, Kiristoci sun yi ɗokin halartar taro don su bauta wa Jehobah kuma su koyi abubuwa game da shi. (Ayyukan Manzanni 2:42) Babu shakka, kai ma kana ɗokin halartan taro. Amma wataƙila halartan taro a kai a kai yana maka wuya. Mai yiwuwa, kana yin sa’o’i da yawa a wajen aiki ko hidimomi sun yi maka yawa, ko kuma kana yawan gajiya. Saboda haka, mene ne zai taimaka mana mu yi iya ƙoƙarinmu don mu halarci taro? [1] (Ka duba ƙarin bayani.) Ta yaya za mu ƙarfafa waɗanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su da kuma wasu mutane su riƙa halartan taro a kai a kai? Wannan talifin zai bayyana dalilan da suka sa halartan taro (1) yake amfanarmu, (2) yake ƙarfafa ‘yan’uwa, da kuma (3) faranta wa Jehobah rai. [2]​—⁠Ka duba ƙarin bayani.

HALARTAN TARO YANA AMFANAR MU

4. Ta yaya halartan taro da ‘yan’uwa yake taimaka mana mu koyi abubuwa game da Jehobah?

4 Muna koyan abubuwa a taro. Muna koyan abubuwa game da Jehobah a kowane taro. Alal misali, ba da daɗewa ba aka kammala nazarin littafin nan Ka Kusaci Jehovah a yawancin ikilisiyoyi a sashen Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Yaya ka ji sa’ad da muke tattauna halayen Jehobah kuma ka saurari kalaman ‘yan’uwa game da shi? Babu shakka, hakan ya sa ka ƙara ƙaunar Jehobah sosai. Muna koyan darussa sa’ad da muka saurari jawabai da gwaji da kuma karatun Littafi Mai Tsarki. (Nehemiya 8:⁠8) Ƙari ga haka, sa’ad da muke shirya karatun Littafi Mai Tsarki kowane mako, muna koyan abubuwa da yawa kuma muna amfana daga ‘yan’uwa yayin da suke bayyana abubuwan da suka koya daga karatun.

5. Ta yaya taro ya taimaka maka ka yi amfani da abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki kuma ka kyautata yadda kake wa’azin bishara?

5 A taronmu, muna koyan yadda za mu yi amfani da darussa daga Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu. (1 Tasalonikawa 4:​9, 10) Shin ka taɓa halartan taron Nazarin Hasumiyar Tsaro kuma ka ji cewa ya kamata ka ƙara ƙwazo a hidimarka ga Jehobah, ko ka kyautata yadda kake addu’a ko kuma ka gafarta wa wani ɗan’uwa ko wata ‘yar’uwa? Taron da muke yi a tsakiyar mako yana taimaka mana mu san yadda za mu yi wa’azin bishara da kuma taimaka wa mutane su koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.​—Matta 28:​19, 20.

6. Ta yaya taronmu yake taimaka mana da kuma ƙarfafa mu?

6 Muna samun ƙarfafa a taro. Yanayi dabam-dabam da muke fuskanta a wannan duniyar da Shaiɗan yake mulki yana iya sa mu sanyin gwiwa ko kuma baƙin ciki. Amma muna samun ƙarfafa don mu ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da muka halarci taro. (Karanta Ayyukan Manzanni 15:​30-32.) A yawancin lokaci, muna tattauna yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika. Hakan yana sa mu tabbata cewa alkawuran da Jehobah ya yi game da nan gaba za su cika. ‘Yan’uwanmu maza da mata suna taimaka mana sa’ad da suka yi kalamai da kuma sa’ad da suka rera waƙoƙi don yabon Jehobah daga zuciyarsu. (1 Korintiyawa 14:26) Muna farin ciki sa’ad da muka yi hira kafin taro da kuma bayan haka don mun san cewa ‘yan’uwanmu abokanmu ne na kud da kud kuma suna ƙaunarmu sosai.​—⁠1 Korintiyawa 16:​17, 18.

7. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa halartan taro?

7 Jehobah yana ba mu ruhunsa mai tsarki sa’ad da muka halarci taro. Yesu yana ja-gorar ikilisiyoyi da ruhu mai tsarki. Ya gaya mana cewa mu ‘ji abin da ruhu ke faɗa wa ikilisiyoyi.’ (Ru’ya ta Yohanna 2:⁠7) Ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu guje wa jaraba kuma mu yi wa’azi da gaba gaɗi. Ƙari ga haka, zai iya taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka dace. Shi ya sa ya wajaba mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance a taro kuma mu amfana daga taimakon ruhu mai tsarki.

MUNA ƘARFAFA ‘YAN’UWANMU A TARO

8. Ta yaya ‘yan’uwa suke amfana sa’ad da muka yi kalamai kuma muka rera waƙa a taro? (Za ka sami ƙarin bayani a akwatin nan “ Yana Farin Ciki Bayan Taro.”)

8 Halartan taro yana ba mu zarafin nuna wa ‘yan’uwa cewa muna ƙaunar su. ‘Yan’uwa da yawa a cikin ikilisiyarmu suna fama da matsaloli masu tsanani sosai. Manzo Bulus ya ce: “Mu . . . riƙa kula da juna.” (Ibraniyawa 10:​24, 25, Littafi Mai Tsarki) Za mu iya nuna cewa muna ƙaunar ‘yan’uwanmu ta wajen kasancewa a taro don mu ƙarfafa juna. Sa’ad da muka halarci taro, muna nuna wa ‘yan’uwanmu cewa muna so mu kasance tare da su kuma mun damu da lafiyarsu. Muna ƙarfafa su sa’ad da muka yi kalamai kuma muka rera waƙoƙi daga zuciyarmu.​—⁠Kolosiyawa 3:⁠16.

9, 10. Ka bayyana yadda abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 10:16 zai taimaka mana mu fahimci muhimmancin halartan taro tare da ‘yan’uwanmu. (b) Idan muna halartan taro a kai a kai, ta yaya za mu taimaka wa ɗan’uwan da ‘yan gidansu suka ƙi shi?

9 Sa’ad da muka halarci taro, muna taimaka wa ‘yan’uwa a ikilisiya su kusaci juna. (Karanta Yohanna 10:16.) Yesu ya kwatanta kansa da makiyayi kuma ya ce mabiyansa suna kamar garken tumaki. Ka yi la’akari da wannan misali: Idan tumaki ba sa tare, a ce biyu suna kan dutse, wasu biyu kuma suna cikin ƙwari kuma ɗaya tana wani wuri dabam, shin za a iya kiran waɗannan tumakin garke guda? Da kyar! Kafin su zama garke guda, wajibi ne su kasance tare kuma su bi makiyayinsu. Hakazalika, idan muka ƙi halartan taro, muna nesa daga ‘yan’uwanmu kuma hakan bai dace ba. Muna bukata mu halarci taro don mu zama “garke ɗaya” kuma mu bi “makiyayi ɗaya.”

10 Taronmu yana taimaka mana mu kasance da haɗin kai kamar iyali. (Zabura 133:⁠1) Wasu Kiristoci da ke halartan taro a ikilisiya suna fuskantar matsaloli don iyayensu da kuma ‘yan’uwansu maza da mata sun yi watsi da su don suna bauta wa Jehobah. Amma Yesu ya yi alkawari cewa zai tanadar musu da iyali da zai ƙaunace su kuma ya kula da su. (Markus 10:​29, 30) Idan kana halartan taro a kai a kai, za ka iya zama kamar uba ko uwa ko ɗan’uwa ko ‘yar’uwar wata a cikin ikilisiya. Yin irin wannan tunanin zai taimaka mana mu yi iya ƙoƙarinmu mu halarci taro.

MUNA FARANTA WA JEHOBAH RAI

11. Ta yaya halartan taro yake taimaka mana mu ba Jehobah abin da ya cancanta a gare shi?

11 Idan muka halarci taro, muna ba wa Jehobah abin da ya cancanta a gare shi. Jehobah ne Mahaliccinmu, ya cancanci mu ɗaukaka shi kuma mu yabe shi. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 7:12.) Za mu iya yin hakan a taro sa’ad da muke addu’a da waƙar yabo ga Jehobah da kuma sa’ad da muke magana game da shi. Hakika, ba ƙaramin gata ba ne muke da shi na bauta wa Jehobah kowane mako!

12. Yaya Jehobah yake ji sa’ad da muka bi umurninsa game da halartan taro?

12 Da yake Jehobah ne ya halicce mu, ya kamata mu bi umurninsa. Ya umurce mu cewa mu riƙa halartan taro da ‘yan’uwanmu, musamman ma yayin da ƙarshen wannan zamanin yake gabatowa. Saboda haka, Jehobah yana farin ciki da mu idan muka bi wannan umurnin. (1 Yohanna 3:22) Yana lura cewa muna sha’awar halartan taro kuma yana ganin ƙoƙarin da muke yi don mu yi hakan.​—⁠Ibraniyawa 6:⁠10.

13, 14. Ta yaya muke kusantar Jehobah da Yesu sa’ad da muka halarci taro?

13 Sa’ad da muka halarci taro, muna nuna wa Jehobah cewa muna so mu kusace shi da kuma Ɗansa. Sa’ad da muka halarci taro, muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma Jehobah yana koya mana abubuwan da za mu yi da kuma yadda ya kamata mu yi rayuwa. (Ishaya 30:​20, 21) Saboda haka, sa’ad da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah suka halarci taronmu, suna gani cewa lalle Jehobah ne yake ja-gorarmu. (1 Korintiyawa 14:​23-25) Jehobah ne yake yi mana ja-gora a taronmu da ruhunsa mai tsaki, kuma shi ne tushen abubuwan da muke koya a taro. Sa’ad da muka halarci taro, tamkar muna sauraron Jehobah ne. Ƙari ga haka, muna shaida yadda yake ƙaunarmu kuma hakan yana sa mu kusace shi.

14 Yesu ne shugaban ikilisiya, ya ce: “Gama wurin da mutum biyu ko uku sun taru cikin sunana, nan ni ke a tsakiyarsu.” (Matta 18:20) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ‘yana tafiya cikin tsakiyar’ ikilisiyoyi. (Ru’ya ta Yohanna 1:20–2:⁠1) A bayyane yake cewa Jehobah da Yesu suna tare da mu kuma suna ƙarfafa mu sa’ad da muka halarci taro. Yaya kake ganin Jehobah yake ji sa’ad da ya lura cewa kana iya ƙoƙarinka don ka kusace shi da kuma Ɗansa?

15. Ta yaya halartan taro yake nuna wa Allah cewa muna so mu yi masa biyayya?

15 Sa’ad da muka halarci taro, muna nuna wa Jehobah cewa muna son bin umurninsa. Jehobah ba ya tilasta mana mu yi abin da yake so. (Ishaya 43:23) Saboda haka, idan muka bi umurninsa game da halartan taro da son ranmu, muna nuna masa cewa muna ƙaunar sa kuma mun gaskata cewa yana da iko ya gaya mana abin da ya kamata mu yi. (Romawa 6:17) Alal misali, mene ne za mu yi idan shugabanmu a wurin aiki ya ba mu aikin da zai hana mu halartan taro a kai a kai? Ko kuma wataƙila, gwamnati ta kafa doka cewa duk wanda ya halarci taron Shaidun Jehobah zai biya diyya ko a jefa shi a cikin kurkuku ko a yi masa wani hukunci mai tsanani sosai. Ko kuma a wani lokaci, mun fi so mu yi wani abu dabam maimakon mu halarci taro. Idan muka sami kanmu a cikin ɗaya daga cikin waɗannan yanayin, wajibi ne mu yanke shawara a kan abin da za mu yi. (Ayyukan Manzanni 5:29) Amma mu tuna cewa a duk lokacin da muka yi wa Jehobah biyayya da son rai, muna faranta masa rai.​—Misalai 27:11.

KADA KA FASA HALARTAR TARO TARE DA ‘YAN’UWANKA

16, 17. (a) Ta yaya muka san cewa Kiristoci na farko sun ɗauki halartan taro da muhimmanci sosai? (b) Mene ne ra’ayin Ɗan’uwa George Gangas game da halartan taron Kirista?

16 Bayan taron da Kiristoci suka yi a shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, Kiristoci sun ci gaba da halartan taro don su bauta wa Jehobah. Suka “lizima a cikin koyarwar manzanni da zumunta.” (Ayyukan Manzanni 2:42) Har ma sa’ad da gwamnatin Roma da kuma shugaban Yahudawa suka soma tsananta musu, ba su fasa halartan taro ba. Ko da yake yin hakan bai kasance musu da sauƙi ba, sun yi iya ƙoƙarinsu su halarci taro tare da ‘yan’uwa.

17 A yau ma, bayin Jehobah suna gode masa don taron da ake gudanarwa kuma suna jin daɗin halartan taron. Wani ɗan’uwa da ya yi shekaru 22 a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah mai suna George Gangas ya ce: “A gare ni, kasancewa a taro tare da ‘yan’uwa abin farin ciki ne sosai da kuma ban ƙarfafa. Ina son zuwa Majami’ar Mulki da wuri kuma na zama mutumin ƙarshe da zai bar wurin, idan ya yiwu. Ina matuƙar farin ciki sa’ad da nake tattaunawa da mutanen Allah. Sa’ad da nake tare da su, ina ji kamar ina tare da iyalina, ina jin daɗin wannan yanayi mai kyau da muke mora.” Ya daɗa cewa: “Babban burina shi ne in kasance a taro.”

18. Mene ne ra’ayinka game da halartan taro, kuma mene ne ka ƙudiri niyyar yi?

18 Shin kana jin daɗin halartan taro don ka bauta wa Jehobah kamar wannan ɗan’uwa? Idan haka ne, ka yi iya ƙoƙarinka don ka riƙa kasancewa da ‘yan’uwa a taro, ko da yin hakan yana da wuya. Ka nuna wa Jehobah cewa ra’ayinka ɗaya ne da Sarki Dauda sa’ad da ya ce: “Ubangiji, ina ƙaunar zaman gidanka.”​—Zabura 26:8.

^ [1] (sakin layi na 3) Wasu ‘yan’uwanmu maza da mata ba sa iya halartan taro a kai a kai don wani mawuyacin yanayi da suke fuskanta. Alal misali, rashin lafiya. Ya kamata su tuna cewa Jehobah ya san yanayinsu kuma yana farin ciki don ƙwazon da suke yi su bauta masa. Dattawa za su iya taimaka wa waɗannan ‘yan’uwa su saurari abubuwan da aka tattauna a taro ta hanyar tarho ko kuma ta ɗaukan jawaban a na’ura don waɗannan ‘yan’uwan su saurara.

^ [2] (sakin layi na 3) Ka duba akwatin nan “ Dalilan da Suka Sa Muke Halartan Taro..”

Muna samun ƙarfafa don mu ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da muka halarci taro

Jehobah yana lura cewa muna sha’awar halartan taro kuma yana ganin ƙoƙarin da muke yi don mu yi hakan