Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Gaya wa Jehobah Damuwarku

Ku Gaya wa Jehobah Damuwarku

“Kuna zuba dukan alhininku a bisansa [Jehobah], domin yana kula da ku.”​—1 BIT. 5:7.

WAƘOƘI: 6023

1, 2. (a) Me ya sa ba za mu yi mamaki ba idan muka sami kanmu a mawuyacin hali? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me za mu bincika a wannan talifin?

MUNA rayuwa a mawuyacin zamani. Shaiɗan yana fushi sosai kuma yana “kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bit. 5:8; R. Yoh. 12:17) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa a wasu lokuta bayin Allah sukan sami kansu a mawuyacin hali. Bayin Allah masu aminci a dā irinsu Sarki Dauda sun sha “wahala.” (Zab. 13:​2, Littafi Mai Tsarki) Manzo Bulus ma ya fuskanci wahala “saboda dukan ikilisiyoyi.” (2 Kor. 11:28) Amma mene ne za mu yi sa’ad da muka sami kanmu a yanayi mai wuya?

2 Ubanmu mai ƙauna ya taimaka wa bayinsa a dā da suka sha wahala kuma muna da tabbaci cewa zai taimaka mana a yau. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kuna zuba dukan alhininku [damuwarku] a bisansa, domin yana kula da ku.” (1 Bit. 5:⁠7) Ta yaya za mu iya yin hakan? Bari mu bincika hanyoyi huɗu da za mu iya yin hakan. Za mu yi hakan ta yin addu’a da karanta Kalmar Allah da yin bimbini. Ƙari ga haka, ka roƙi Allah ya ba ka ruhu mai tsarki kuma ka gaya wa amininka damuwarka. Yayin da kake bincika waɗannan hanyoyi huɗun, ka ga ko za ka iya ɗaukan wasu matakai don ka kyautata rayuwarka.

KA GAYA WA JEHOBAH DAMUWARKA

3. Ta yaya za ka “zuba nawayarka bisa Ubangiji” ko kuma ka gaya masa damuwarka?

3 Abu na farko da za mu yi shi ne yin addu’a ga Jehobah. A lokacin da kake fuskantar wasu matsalolin da suka sa ka cikin wani irin mawuyacin hali, ka yi addu’a ga Allah. Dauda ya yi addu’a ga Jehobah ya ce: “Ka kasa kunne ga addu’ata, ya Allah.” Sai ya ƙara da cewa: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka.” (Zab. 55:​1, 22) Bayan ka yi iya ƙoƙarinka don ka magance matsalar, zai dace ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka rage yin alhini ko damuwa. Amma ta yaya addu’a za ta taimaka maka ka daina damuwa ainun saboda matsalarka?​—⁠Zab. 94:​18, 19.

4. Me ya sa addu’a take da muhimmanci sa’ad da muke alhini ko wahala?

4 Karanta Filibiyawa 4:​6, 7Idan muka yi addu’a ga Jehobah kuma muka nace a yin hakan, Jehobah zai taimaka mana. Ta yaya zai yi hakan? Zai taimaka mana mu sami kwanciyar hankali kuma mu rage damuwa. ‘Yan’uwa da yawa a cikinmu sun shaida hakan. Maimakon su riƙa damuwa da tsoro saboda abubuwan da suke fuskanta, Allah ya taimaka musu su kasance da salama da kwanciyar hankali. Kai ma za ka iya shaida hakan. Saboda haka, ‘salama ta Allah’ za ta iya taimaka maka ka shawo kan kowace matsala. Babu shakka, za ka iya tabbata da wannan alkawarin cewa: “Kada ka yi fargaba; gama ni ne Allahnka: ni ƙarfafa ka: ni taimake ka.”​—⁠Isha. 41:⁠10.

SAMUN KWANCIYAR HANKALI DAGA KALMAR ALLAH

5. Ta yaya Kalmar Allah za ta taimaka mana mu kasance da salama ko kwanciyar hankali?

5 Abu na biyu da za mu yi don mu sami kwanciyar hankali shi ne karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta. Me ya sa yin hakan yake da muhimmanci? Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawarwari masu kyau da za su taimaka mana sa’ad da muke alhini ko kuma damuwa. Kalmar Allah tana taimaka mana sosai don tana ɗauke da wasu abubuwan da za su taimaka mana mu kasance da hikima. Za ka sami ƙarfafa sosai idan kana bimbini a kan Kalmar Allah dare da rana don ka san yadda za ka yi amfani da abin da kake koya. Jehobah ya ce idan muna karanta Kalmarsa za mu “ƙarfafa” kuma mu kasance da “ƙarfin zuciya” ba masu tsoro ko “fargaba” ba.​—Josh. 1:​7-9.

6. A wace hanya ce kalamin Yesu zai taimaka maka?

6 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da furucin Yesu da ya ƙarfafa mutane. Kalaminsa da koyarwarsa sun ƙarfafa mutane sosai. Mutane da yawa sun saurari Yesu don kalaminsa ya sa sun sami kwanciyar hankali kuma ya ƙarfafa waɗanda suka raunana. (Karanta Matta 11:​28-30.) Ya bi da mutane yadda ya dace. (Mar. 6:​30-32) Hakazalika, zai iya taimaka mana a yau kamar yadda ya taimaka wa manzanninsa a dā. Ba sai ka kasance tare da Yesu a zahiri kafin ka amfana daga hakan ba. Da yake Yesu yana sarauta a sama zai ci gaba da taimaka wa mutane. Don haka, sa’ad da kake da damuwa, zai iya ‘taimaka’ maka a lokacin da ya dace. Babu shakka, Yesu zai taimaka maka sa’ad da kake shan wahala kuma zai sa ka kasance da bege da kuma ƙarfin hali.​—Ibran. 2:​17, 18; 4:16.

HALAYEN ALLAH DA RUHU MAI TSARKI YAKE SA MU KASANCE DA SU

7. Ta yaya za ka amfana sa’ad Allah ya amsa roƙonka na neman ruhu mai tsarki?

7 Yesu ya yi alkawari cewa Ubanmu na sama zai ci gaba da tanadar da ruhu mai tsarki ga bayinsa da suke neman taimakonsa. (Luk. 11:​10-13) Hakan zai sa mu tattauna abu na uku da zai taimaka mana sa’ad da muke alhini ko damuwa. Ruhu mai tsarki ko kuma ikon da Allah yake amfani da shi zai taimaka mana mu kasance da halaye irin na Allah. (Karanta Galatiyawa 5:​22, 23; Kol. 3:10) Idan ka ci gaba da koyan waɗannan fannoni dabam-dabam na ‘yar ruhu, dangantakarka da Jehobah za ta yi ƙarfi. Ban da haka ma, za ka guji wasu yanayin da za su iya sa ka sami kanka a wani hali. Bari mu bincika yadda ‘yar ruhu za ta taimaka mana a wasu hanyoyi.

8-12. Ta yaya ‘yar ruhu mai tsarki za ta taimaka maka ka bi da wasu mawuyacin yanayi kuma ka guje su?

8 ‘Kauna da farin ciki da salama.’ Idan ka yi ƙoƙari ka bi da mutane da ladabi, hakan zai taimaka maka ka rage alhini ko damuwa. Ta yaya? Idan kana ƙaunar ‘yan’uwa kuma kana girmama su, za ka guji wasu abubuwan da za su sa ka cikin matsala.​—⁠Rom. 12:⁠10.

9 ‘Tsawon jimrewa da nasiha da kuma nagarta.’ Za ka kasance da salama da ‘yan’uwanka idan ka bi wannan shawarar: “Ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara.” (Afis. 4:32) Hakan zai sa ka guji wasu abubuwan da za su sa ka ɗawainiya. Ƙari ga haka, hakan zai taimaka maka ka bi da wasu yanayi da muke fuskanta saboda ajizancinmu.

10 “Aminci” ko bangaskiya. A yau, muna yawan damuwa ne domin matsalar kuɗi ko dukiya. (Mis. 18:11) Amma idan muka kasance da bangaskiya cewa Jehobah yana ƙaunarmu, hakan zai taimaka mana mu guji ɗawainiya ko alhini. Ta yaya? Bin gargaɗin Bulus cewa mu ‘haƙura da abin da muke da shi’ zai taimaka mana. Bulus ya ƙara cewa: “Gama shi [Allah] da kansa ya ce, daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba. Domin wannan fa gaba gaɗi muna cewa, Ubangiji mai-taimakona ne; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum zai mini?”​—Ibran. 13:​5, 6.

11 ‘Tawali’u da kamewa.’ Ka yi tunanin irin amfanin da za ka samu idan ka bi wannan shawarar. Hakan zai taimaka maka ka guji wasu yanayin da za su iya sa ka cikin wani hali. Za ka iya guje wa halaye kamar su “ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage.”​—⁠Afis. 4:⁠31.

12 A gaskiya, kana bukatar tawali’u don ka kasance cikin “hannu mai-iko na Allah” kuma ka ‘zuba dukan alhininka a bisansa.’ (1 Bit. 5:​6, 7) Amma idan ka kasance da tawali’u, Allah zai taimaka maka kuma ya nuna maka alheri. (Mi. 6:⁠8) Hakan zai taimaka maka ka dogara ga Jehobah. Ƙari ga haka, za ka iya shawo kan ɗawainiya idan ka lura da yadda Allah yake ƙaunar ka da kuma taimaka maka.

“KADA FA KU YI ALHINI”

13. Mene ne Yesu yake nufi da ya ce: “Kada fa ku yi alhini”?

13 A littafin Matta 6:34 (karanta), Yesu ya ba da wannan shawarar: “Kada fa ku yi alhini.” Yakan yi mana wuya mu bi wannan shawarar. Amma, me Yesu yake nufi da ya ce: “Kada fa ku yi alhini”? Hakika, ba ya nufin cewa wanda yake bauta wa Allah ba zai yi alhini ba, domin mun riga mun ga abin da Dauda da Bulus suka faɗa a kan wannan batun. Maimakon haka, Yesu yana gaya wa almajiransa cewa yawan alhini ba zai magance matsalolinsu ba. Ƙari ga haka, Kiristoci za su fuskanci matsaloli a kowace rana, saboda haka, bai kamata su riƙa damuwa ba ta wajen yin tunanin abin da ya faru a dā da kuma abin da zai faru a nan gaba. Ta yaya bin shawarar Yesu zai taimaka maka ka guji alhini?

14. Mene ne za ka yi idan kana yawan tunanin don abin da ka yi a dā?

14 A wasu lokatai, mutane suna damuwa don kuskure da suka yi a dā. Sukan yi tunani sosai domin abin da suka yi ko da yake hakan ya yi shekaru da yawa. A wani lokaci Sarki Dauda ya ga cewa ‘kurakuransa sun sha kansa.’ Ya ce: “Na yi ruri domin rashin kwanciyar zuciyata.” (Zab. 38:​3, 4, 8, 18) Mene ne ya kamata Dauda ya yi a irin wannan yanayin? Mene ne ya yi? Ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai nuna masa jin ƙai kuma ya gafarta masa. Ya faɗi hakan da tabbaci cewa: “Mai albarka ne mutum wanda an gafarta masa laifinsa.”​—Karanta Zabura 32:​1-3, 5.

15. (a) Me ya sa ba ka bukatar ka riƙa damuwa game da abin da ke faruwa a yanzu? (b) Wane mataki ne za ka ɗauka don ka rage alhini? (Ka duba akwatin nan “ Wasu Abubuwan da Za Ka Iya Yi Don Ka Rage Alhini.”)

15 A wani lokaci, za ka iya damuwa da abubuwan da ke faruwa a yanzu. Alal misali, a lokacin da Dauda ya rubuta Zabura ta 55 yana jin tsoro cewa za a kashe shi. (Zab. 55:​2-5) Duk da haka, bai bar alhini ya sa ya daina dogara ga Jehobah ba. Dauda ya yi addu’a don matsalolin da yake fuskanta, amma ya san cewa yana bukatar ya ɗauki mataki don ya bi da abubuwan da suke sa shi alhini. (2 Sam. 15:​30-34) Za ka iya koyon darasi daga wurin Dauda. Maimakon ka bar alhini ya shawo kanka, ka ɗauki mataki don ka bi da yanayin yadda ya dace kuma ka tabbata cewa Jehobah zai kula da kai.

16. Ta yaya sanin ma’anar sunan Allah zai iya ƙarfafa bangaskiyarka?

16 A wasu lokatai, mutum yakan damu da matsalolin da zai iya fuskanta a nan gaba. Amma bai kamata mu riƙa damuwa da abubuwan da ba su faru ba tukuna. Me ya sa? Domin a wasu lokatai abubuwa ba sa taɓarɓarewa yadda muke ganin za su yi. Ƙari ga haka, babu yanayin da zai fi ƙarfin Allah wanda za ka iya gaya wa duk abin da yake damunka. A cikin juyin New World Translation sunansa yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” (Fit. 3:14) Ma’anar wannan sunan ta tabbatar mana cewa Allah zai iya cika nufinsa a madadin bayinsa. Ka kasance da tabbaci cewa Allah zai albarkaci bayinsa masu aminci kuma zai taimaka musu su daina damuwa don abin da suka yi a dā da abin da yake faruwa a yanzu da abin da zai faru a nan gaba.

KA GAYA WA WANI ABIN DA KE DAMUNKA

17, 18. Ta yaya tattaunawa da wasu zai taimaka maka ka rage alhini?

17 Abu na huɗu da zai taimaka maka ka bi da alhini shi ne gaya wa wanda ka amince da shi abin da yake damunka. Matarka ko mijinki ko amininka ko kuma wani dattijo a ikilisiya zai taimaka maka ka bi da yanayinka yadda ya dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nawaya a zuciyar mutum takan sa ta sunkuya: amma maganar alheri takan farantar da ita.” (Mis. 12:25) Tattaunawa da wani zai taimaka maka ka fahimci damuwarka kuma ka shawo kanta. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wurin da babu shawara, nufe nufe sukan warware: Amma cikin taron masu-shawara sukan tabbata.”​—⁠Mis. 15:⁠22.

18 Jehobah yana yin amfani da taron ikilisiya da muke yi a kowane mako don ya taimaka wa Kiristoci su bi da alhini. A wurin kana iya yin cuɗanya da ‘yan’uwa da suka damu da kai kuma suna son su riƙa ƙarfafa juna. (Ibran. 10:​24, 25) Irin wannan “ƙarfafawa” zai sa ya yi maka sauƙi ka shawo kan kowane alhini da kake yi.​—Rom. 1:12.

DANGANTAKARKA DA ALLAH NE ZA TA FI ƘARFAFA KA

19. Me ya sa za ka iya kasancewa da tabbaci cewa dangantakarka da Allah zai ƙarfafa ka?

19 Ka yi la’akari da yadda wani dattijo a ƙasar Kanada ya koyi cewa yana da muhimmanci ya gaya wa Jehobah damuwarsa. Shi malami ne, ban da haka yana rashin lafiya da ke sa shi alhini. Mene ne ya taimaka ma wannan ɗan’uwan? Ya ce: “Na yi ƙoƙari sosai in ƙarfafa dangantaka ta da Jehobah, kuma hakan ya taimaka mini in jimre da matsaloli da nake fuskanta. Aminai da ‘yan’uwa a ikilisiya sun taimaka mini sosai. Ƙari ga haka, nakan gaya wa matata yadda nake ji. Dattawan ikilisiyarmu da mai kula da da’ira sun taimaka mini in ga yanayina yadda Jehobah yake ganin yanayin. Wani likita ya taimaka mini na fahimci yanayina, kuma na tsara yadda nake amfani da lokaci na. Na keɓe lokacin hutawa da kuma motsa jiki. A hankali sai na koyi yadda zan bi da yanayina da kuma yadda nake ji. Ƙari ga haka, nakan dogara ga Jehobah ya taimake ni idan ina cikin yanayin da ban san yadda zan bi da shi ba.”

20. (a) Ta yaya za mu gaya wa Allah dukan abin da yake damunmu? (b) Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

20 A wannan talifin, mun koyi cewa yana da muhimmanci mu gaya wa Allah duk abin da ke damunmu sa’ad da muke addu’a da karanta Kalmarsa da kuma yin bimbini a kanta. Ƙari ga haka, mun tattauna yadda za mu amfana idan muka roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. Kuma mun koya cewa za mu iya gaya wa amininmu abin da ke damunmu kuma mu halarci taron ikilisiya. A talifi na gaba za a tattauna yadda Jehobah yake kula da mu ta wajen sa mu kasance da begen samun albarka.​—Ibran. 11:6.