Ka Sani?
Ta yaya ake ɗaukan wuta a zamanin dā?
LITTAFIN Farawa 22:6 ya ce Ibrahim ya yi shiri don miƙa hadaya a wani wuri kuma ya “ɗauki itace domin hadaya ta ƙonawa, ya aza ma Ishaƙu ɗansa; a cikin hannunsa kuwa yana riƙe da wuta da wuƙa; duka biyunsu suka tafi tare.”
Littafi Mai Tsarki bai ambata yadda ake kunna wuta a zamanin dā ba. Amma wani masani ya gaskata cewa “ba zai yiwu a ce sun ɗauki wutar har zuwa inda suka je ba.” Maimakon haka, wataƙila Ibrahim ya tafi da abin da zai kunna wutar da shi.
Amma wasu sun ce kunna wuta a zamanin dā yana da wuya. Saboda haka, ya fi sauƙi mutane su ɗebi garwashi daga maƙwabtansu maimakon su kunna wutar da kansu. Masana da yawa sun gaskata cewa Ibrahim ya ɗauki kasko ko kwano da ke ɗauke da gawayi ko garwashi da suka yi amfani da shi daddare. (Isha. 30:14) Za a iya yin tafiya mai nisa da garwashin wuta kuma idan ana so a yi amfani da wuta sai a saka itace.