1 | Adduꞌa—“Ku Danka Masa Dukan Damuwarku”
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ku danƙa masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”—1 BITRUS 5:7.
Abin da Hakan Yake Nufi
Jehobah ya ce mu gaya masa duk abin da yake damunmu. (Zabura 55:22) Babu matsalar da ba za mu iya yin adduꞌa a kai ba. Idan abin da yake damunmu yana da muhimmanci a gare mu, Jehobah zai ɗauke shi da muhimmanci. Yin adduꞌa zai taimaka mana mu kasance da kwanciyar hankali.—Filibiyawa 4:6, 7.
Yadda Yin Hakan Zai Taimaka
Idan muna fama da matsalar ƙwaƙwalwa, za mu ji kamar mun kaɗaita. Ba kowane lokaci ne mutane suke fahimtar yanayin da muke ciki ba. (Karin Magana 14:10) Amma idan muka yi adduꞌa kuma muka gaya wa Jehobah yadda muke ji, zai tausaya mana kuma ya san abin da muke fama da shi. Jehobah yana ganin duk famar da muke yi kuma ya san dukan damuwarmu, yana so mu yi adduꞌa mu gaya masa duk abin da yake damunmu.—2 Tarihi 6:29, 30.
Idan mun gaya wa Jehobah abin da ke damunmu, hakan yana sa mu kasance da tabbaci cewa ya damu da mu. Idan muka yi haka, mu ma za mu ji kamar wani marubucin Zabura da ya yi adduꞌa cewa: “Ka ga wahalata, ka san damuwar zuciyata.” (Zabura 31:7) Sanin cewa Jehobah yana ganin abubuwan da muke fama da su, zai taimaka mana mu jimre yanayoyi masu wuya. Amma ba ganin matsalolin kawai yake yi ba. Babu wanda ya kai Jehobah fahimtar abin da muke ciki kuma zai taimaka mana mu sami ƙarfafar da muke bukata daga Littafi Mai Tsarki.