Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA MU JIMRE SA’AD DA WANI YA RASU

Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?

Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?

Ka tuna matar da muka ambata ɗazun mai suna Gail da maigidanta ya rasu? Ta ɗauka cewa ba zai yiwu ta daina makokin maigidanta mai suna Rob ba. Amma, tana so ta ga an ta da maigidanta kamar yadda Allah ya yi alkawari zai yi a nan gaba. Ta ce: “Nassin da na fi so shi ne Ru’ya ta Yohanna 21:​3, 4.” Wurin ya ce: “Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su . . . zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”

Gail ta ce: “Wannan alkawari ne mai kyau. Nakan tausaya wa mutanen da suke makoki amma ba su san da wannan alkawarin ba.” Gail ta soma wa’azi da ƙwazo don ta taimaka wa mutane su yi begen cewa nan ba da daɗewa ba, ‘mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.’

Ayuba ya tabbata cewa zai sake rayuwa

Za ka iya ce, ‘Hakan na da wuya.’ Amma ka yi la’akari da misalin wani mutum mai suna Ayuba. Ya yi fama da wata cuta mai tsanani. (Ayuba 2:⁠7) Ya ji kamar gara da a ce ya mutu, duk da haka, yana da bege cewa ko da ya mutu Allah zai ta da shi. Ya ce da gaba gaɗi: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira [wato Kabari], ka ɓoye ni . . . Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.” (Ayuba 14:​13, 15) Ayuba ya tabbata cewa Allah zai yi marmarin ta da shi.

Nan ba da daɗewa ba a lokacin da duniya za ta zama aljanna, Allah zai ta da Ayuba da kuma mutane da yawa da suka kasance da aminci. (Luka 23:​42, 43) Littafin Ayyukan Manzanni 24:15 ya tabbatar da hakan, wurin ya ce: “Za a yi tashin matattu.” Yesu ma ya ce: “Kada ku yi mamakin wannan; gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.” (Yohanna 5:​28, 29) Ayuba zai ga cikar ayar nan, zai sake komawa cikin ‘ƙuruciya’ kuma fatarsa za ta “fi na yaro sabontaka.” (Ayuba 33:​24, 25) Babu shakka, abin da zai faru da dukan amintattun bayin Allah ke nan a duniya.

Idan wani naka ya rasu, babu mamaki abin da muka tattauna ba zai sa ka daina makokin gabaki ɗaya ba. Amma yin bimbini a kan alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka zama da bege da kuma ƙarfin ci gaba da rayuwa.​—1 Tasalonikawa 4:13.

Za ka so ka samu ƙarin bayani a kan abin da zai taimake ka sa’ad da kake makoki? Ko kana da wata tambaya kamar, “Me ya sa Allah ya ƙyale mugunta da wahala?” Don Allah, ka shiga dandalinmu na jw.org/⁠ha don ka ga amsoshi masu ban ƙarfafa da ke cikin Littafi Mai Tsarki.