Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yin rantsuwa?
Rantsuwa “wani abu mai muhimmanci ne da ya ƙunshi alkawarin yin wani abu kuma a yawancin lokuta, mai yin rantsuwar yakan kira sunan Allah . . . a matsayin shaida.” Ana iya faɗinsa da baki ko a rubuta shi.
Wasu za su iya cewa yin rantsuwa laifi ne domin Yesu ya ce: “Kada ma ku rantse sam . . . Abin da duk za ku faɗa, ya tsaya kan ‘I’ ko ‘A’a’ kawai. In dai ya zarce haka, daga Mugun ya fito.” (Mat. 5:33-37, Mai Makamantu Ayoyi) Hakika Yesu ya san cewa Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa ya bukaci a yi rantsuwa a wasu lokuta kuma wasu bayin Allah ma sun yi rantsuwa. (Far. 14:22, 23; Fit. 22:10, 11) Ya kuma san cewa Jehobah da kansa ma ya yi rantsuwa. (Ibran. 6:13-17) Saboda haka, Yesu ba ya nufin cewa bai kamata mu yi rantsuwa ba sam-sam. A maimakon haka, yana magana ne game da rantsuwar da ake yi a kan abubuwa marasa muhimmanci. Ya kamata mu ɗauki cika alkawarinmu a matsayin ibada. Don haka, dole ne mu yi abin da mun yi rantsuwa a kai.
Me ya kamata ka yi idan aka ce ka yi rantsuwa? Da farko, ka tabbata cewa za ka iya cika alkawarinka. Idan ba ka tabbata ba, gwamma kada ka yi rantsuwar. Kalmar Allah ta yi mana gargaɗi cewa: “Gwamma kada ka yi rantsuwa, da a ce ka yi rantsuwa amma ba ka cika ba.” (M. Wa. 5:5) Bayan haka, ka yi tunanin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka shafi yin rantsuwar. Sai ka yanke shawarar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ba za ta dami zuciyarka ba. Waɗanne ƙa’idodi ne muke magana a kai?
Wasu rantsuwa sun jitu da nufin Allah. Alal misali, Shaidun Jehobah suna yi wa juna alkawari a lokacin da ake so a haɗa musu aure. Wannan alkawarin ma rantsuwa ne. A gaban Allah da kuma shaidu, mata da miji da za su yi aure za su yi alkawari cewa za su ƙaunaci juna kuma za su daraja juna “har iyakar rayuwarsu.” (Wasu ma’aurata ba za su yi amfani da kalmomin nan kamar yadda suke a nan ba, duk da haka, suna yi wa juna alkawari a gaban Allah.) Bayan haka za su zama mata da miji kuma bai kamata aurensu ya rabu ba. (Far. 2:24; 1 Kor. 7:39) Wannan tsarin ya dace kuma ya jitu da nufin Allah.
Wasu rantsuwa ba su jitu da nufin Allah ba. Kirista na gaskiya ba zai yi rantsuwa cewa zai musanta imaninsa ko kuma ya yi amfani da makami ya kāre ƙasarsa ba. Yin hakan ba zai jitu da dokokin Allah ba. Ya kamata Kiristoci su zama “ba na duniya ba.” Saboda haka, babu ruwanmu da yaƙe-yaƙe da kuma gardama da ake yi a ƙasashe.—Yoh. 15:19; Isha. 2:4; Yak. 1:27.
Luk. 20:25.
Kirista ne zai zaɓi ko zuciyarsa za ta yarda masa ya yi wasu irin rantsuwa. A wasu lokuta, za mu bukaci mu yi tunani sosai a kan rantsuwar saboda gargaɗi da Yesu ya bayar cewa ‘mu ba Kaisar abin da yake na Kaisar, mu kuma ba Allah abin da yake na Allah.’—A ce wani Kirista yana so ya cika fom na zama ɗan ƙasa, ko kuma a ba shi fasfo na ƙasar, sai aka bukace shi ya yi rantsuwa cewa zai yi biyayya ga ƙasar. Idan irin wannan rantsuwar a ƙasar ta ƙunshi yin abin da ya saɓa wa dokokin Allah, zuciyarsa ba za ta yarda masa ya yi rantsuwar ba. Amma gwamnatin ƙasar za ta iya yarda masa ya canja wasu abubuwa a rantsuwar domin zuciyarsa ta bar shi ya yi rantsuwar.
Yin rantsuwar biyayya ga ƙasa da aka canja wasu abubuwa a cikin rantsuwar ya jitu da abin da ke Romawa 13:1, inda Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dole ne kowa ya yi biyayya ga shugabannin gwamnati.” Saboda haka, Kirista zai iya zaɓa ya yi rantsuwa cewa zai yi wani abin da Allah ya riga ya bukace shi ya yi da yake hakan ba laifi ba ne.
Idan aka ce mu yi amfani da wani abu ko mu yi wata alama yayin da muke rantsuwa, muna bukatar mu yi abin da zai jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ba zai dami zuciyarmu ba. Mutanen Roma da Scythia sukan yi amfani da takubansu yayin da suke rantsuwa kuma hakan yana nufin suna amfani da wannan alamar allah na yaƙi don su nuna cewa mutumin yana faɗin gaskiya ne. Helenawa kuma sukan ɗaga hannu sama yayin da suke rantsuwa. Ta hakan, suna nuna cewa sun yarda akwai allah da yake gani da kuma jin abin da suke yi, wanda ’yan Adam za su ba shi lissafin yadda suka yi amfani da rayuwarsu.
Hakika, bawan Allah ba zai yi rantsuwa da wani abin da ke ɗaukaka ƙasa da ke da alaƙa da bauta ta ƙarya ba. Amma a kotu idan aka ce maka ka saka hannunka a kan Littafi Mai Tsarki kuma ka yi rantsuwa cewa za ka faɗi gaskiya fa? A wannan yanayin, za ka iya zaɓa cewa za ka yi hakan, don Littafi Mai Tsarki ya ambata bayin Allah masu aminci da suka yi wata alama sa’ad da suke rantsuwa. (Far. 24:2, 3, 9; 47:29-31) Yana da muhimmanci ka tuna cewa idan ka yi irin wannan rantsuwar, kana rantsuwa ne a gaban Allah cewa za ka faɗi gaskiya. Ya kamata ka kasance a shirye don ka faɗi gaskiya a duk tambayoyin da za a yi maka.
Da yake muna daraja dangantakarmu da Jehobah, ya kamata mu yi addu’a kuma mu yi tunani da kyau kafin mu yi wata rantsuwa kuma mu tabbata cewa rantsuwar da za mu yi ba za ta sa mu taka ƙa’idodin Allah ko ta dami zuciyarmu ba. Idan ka zaɓi ka yi rantsuwa, dole ne ka yi abin da ka rantse cewa za ka yi.—1 Bit. 2:12.