Ka Sani?
Me ya sa Isra’ilawa a zamanin dā suke biyan sadaki?
A ZAMANIN dā, akan biya iyayen amarya sadaki bayan iyayenta da na saurayinta sun yarda a yi musu aure. A wasu lokuta, sukan yi amfani da dabbobi ko kuɗi ko kuma wasu abubuwa masu daraja don biyan sadaki. A wasu lokuta kuma, saurayin yakan yi wa surukinsa aiki a madadin kuɗin sadakin, kamar yadda Yakubu ya yi wa mahaifin Rahila aiki na shekaru bakwai don ya samu ya aure ta. (Far. 29:17, 18, 20, Mai Makamantu Ayoyi) Me ya sa ake biyan sadaki?
Wani masanin Littafi Mai Tsarki mai suna Carol Meyers ya ce: “Ana biyan iyayen budurwa sadaki ne domin bayan auren, ba za ta ci gaba da yi musu aiki ba kuma hakan zai shafi iyalinta musamman idan su manoma ne.” Ban da haka, wataƙila suna biyan sadakin ne domin su ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin iyalin budurwar da na saurayin. Iyalan suna iya taimaka wa juna a lokacin bukata. Ƙari ga haka, sadakin yana nuna cewa budurwar ta riga ta yi alkawarin auran wani kuma za ta fita daga ƙarƙashin kulawar mahaifinta ta shiga na mijinta.
Biyan sadaki ba ya nufin an sayi budurwar ne ko kuma an sayar da ita. Littafin nan Ancient Israel—Its Life and Institutions ya ce: “Da yake ya zama dole ne a biya iyalin budurwar kuɗin sadaki ko kuma wani abu a madadin kuɗin, yin haka a ƙasar Isra’ila ya yi kamar an sayar da budurwar ne. Amma da alama kuɗin sadaki da ake ba wa iyayen budurwar diyya ne ba sayan ta ake yi ba.”
A wasu ƙasashe a yau, mutane suna bin wannan al’ada na biyan kuɗin sadaki. Idan iyaye Kiristoci suka ce a biya sadaki, zai dace su nuna “sanin yakamata” ta wajen guje wa bukatar kuɗin da zai fi ƙarfin saurayin. (Filib. 4:5, New World Translation; 1 Kor. 10:32, 33) Ta yin hakan, za su nuna cewa su ba masu “son kuɗi” ko haɗama ba ne. (2 Tim. 3:2) Ƙari ga haka, idan iyaye Kiristoci suka bukaci saurayi ya biya kuɗin sadaki mai yawa, hakan zai iya sa ya ɗage auren garin neman kuɗin biyan sadakin. Ko kuma ya daina hidimar majagaba domin yana so ya yi aiki na cikakken lokaci don ya sami kuɗin biyan sadaki mai yawa da aka sa masa.
A wasu ƙasashe, gwamnati ce take saka adadin kuɗin da za a biya sadaki. Idan haka ne, iyaye Kiristoci suna bukatar su bi wannan dokar. Me ya sa? Domin Kalmar Allah ta umurci Kiristoci cewa su “yi biyayya ga shugabannin gwamnati” ta wajen bin dokokin da suka kafa da ba su saɓa wa ƙa’idodin Allah ba.—Rom. 13:1; A. M. 5:29.