Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Jure Saboda Kaunata ta Fari

Na Jure Saboda Kaunata ta Fari

NI SOJA ne ɗan shekara 20 kuma ina rashin lafiya don na kamu da wata muguwar cuta. Saboda haka, a tsakiyar shekara ta 1970, na sami kaina a wani asibiti da ake kira Valley Forge General Hospital, a garin Phoenixville, Pennsylvania da ke Amirka. A kowane minti talatin, wani nas yana auna ƙarfin jinina. Nas ɗin ya girme ni da ’yan shekaru amma ya damu don ƙarfin jinina yana raguwa, sai na tambaye shi, “Mutum bai taɓa mutuwa a idonka ba ko?” Sai ya ce, “e” kuma fuskarsa ta canja don ya tsorata.

A wannan lokacin, ban sa rai zan rayu ba. To, yaya aka yi na sami kaina a asibiti? Bari in ba ka labari.

YADDA NA SOMA AIKI DA YA SHAFI YAƘI

Na soma rashin lafiya sa’ad da nake taimakawa a ɗakin tiyata a lokacin yaƙin Vietnam. Ina son taimaka wa marasa lafiya da waɗanda suka jikkata kuma ina da burin zama likita mai fiɗa. A watan Yuli na shekara ta 1969, na je ƙasar Vietnam. Kamar sauran sababbi, an nuna mini yadda ake yin wasu abubuwa don in saba da yanayi da kuma irin zafin da ake yi a ƙasar.

Jim kaɗan bayan na soma aiki a asibitin fiɗa a Mekong Delta da ke sansanin Dong Tam, jirage masu sauƙar ungulu sun kawo mutane da yawa da suka jikkata. Burina shi ne in soma aiki ba tare da ɓata lokaci ba, da yake ni mai kishin ƙasa ne kuma ina son aiki. An shirya waɗanda suka jikkata kuma aka shigar da su cikin gidajen tirela masu iyakwandishan, wato inda aka tsara don yin tiyata. Ma’aikata da suka yi cunkoso a wannan ƙaramin ɗakin tiyata sun ƙunshi likita mai fiɗa da mai ba da allurar barci da nas mai tsabtace jikin majiyyatan da kuma nas mai ba da kayan aiki, kuma suna iya ƙoƙarinsu don su ceci rayukan mutane. Na lura cewa akwai wasu kayayyaki a cikin baƙaƙƙen jakuna da ba a sauƙar daga jiragen ba. An gaya mini cewa gaɓaɓuwan jikin sojoji da bam ya tarwatsa a bakin dāga ne ke cikin jakunan. A wannan lokacin ne na soma aiki da ya shafi yaƙi.

YADDA NA SOMA BIƊAN ALLAH

Sa’ad da nake karami, na saurari Shaidun Jehobah kuma na san wasu abubuwa da suke koyarwa

Sa’ad da nake ƙarami, na saurari Shaidun Jehobah kuma na san wasu abubuwa da suke koyarwa. Hakan ya faru ne sa’ad da suke nazarin Littafi Mai Tsarki da mahaifiyata, amma ba ta zo ta yi baftisma ba. Ina kasancewa tare da mahaifiyata sa’ad da suke nazari da ita kuma ina jin daɗin nazarin sosai. Akwai ranar da ni da mijin mahaifiyata muke wucewa kusa da Majami’ar Mulki. Sai na tambaye shi, “Me ake yi a nan?” Ya ce: “Kada ka kuskura ka je kusa da mutanen nan!” Na bi shawararsa da yake ina ƙaunarsa kuma na yarda da shi. Bayan haka, ban sake haɗuwa da Shaidun Jehobah ba.

Bayan na dawo daga ƙasar Vietnam, sai na soma tunanin yadda zan soma bauta wa Allah. Abubuwan masu ta da hankali da na shaida a Vietnam sun mamaye tunanina. Kamar dai ba wanda ya fahimci ainihin abin da yake faruwa a Vietnam. Na tuna da zanga-zanga da aka yi saboda rahotannin da ake samu cewa ana kashe yara ƙanana a yaƙi. Masu zanga-zangan suna cewa sojojin Amirka masu kisan yara ƙanana ne.

Da yake ina son bauta wa Allah, sai na soma zuwa coci dabam-dabam. Amma ban ji daɗin abubuwan da na ji da kuma gani a coci ba. Saboda haka, a ranar Lahadi a watan Fabrairu na shekara ta 1971, na halarci taro a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah a garin Delray Beach da ke jihar Florida.

Sa’ad da na shiga, an kusan gama jawabi ga jama’a, sai na zauna na jira nazarin Hasumiyar Tsaro da zai biyo baya. Ko da yake, ban tuna abin da aka tattauna ba, amma na tuna yadda yara ƙanana suna buɗe shafuffukan Littafi Mai Tsarki don karanta nassi. Hakan ya burge ni sosai! Sai na yi shiru ina ta lura da abin da ke faruwa. Yayin da nake fita daga Majami’ar Mulkin, sai wani ɗan’uwa da ya kai wajen shekara 80 mai suna Jim Gardner ya zo ya same ni. Ya miƙa mini wani littafi mai jigo Gaskiya da ke Bishe Zuwa Rai Madawwami kuma ya ce, “Za ka so wannan littafin?” Bayan haka, sai muka shirya ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni a ranar Alhamis da safe.

A daren Lahadin, na je aiki. A lokacin ina aiki a wani asibiti mai zaman kansa a Birnin Boca Raton, a jihar Florida, ina aiki a ɗakin da ake jinyar gaggawa. Ina soma aiki daga ƙarfe 11:00 na dare zuwa ƙarfe 7:00  na safe. Da yake ko’ina ya yi shiru a daren, sai na soma karanta littafin Gaskiya da ke Bishe Zuwa Rai Madawwami. Sai wata nas ta zo ta ƙwace littafin daga hannuna ta duba bangon littafin kuma ta ce: ‘Kai ma kana so ka zama Mashaidin Jehobah ko?’ Sai na ƙwace littafin daga hannunta na ce, “Da alama ko da yake ban gama karanta littafin ba.” Bayan haka, ta ƙyale ni kuma na karance littafin a daren.

Ɗan’uwa Jim Gardner ne ya koya mini Littafi Mai Tsarki kuma shi shafaffe ne da ya san Ɗan’uwa Charles Taze Russell

A lokacin da Ɗan’uwa Gardner yake so ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, sai na tambaye shi, “Yanzu, da wane littafi ne za mu yi nazari?” Ya ce, “Littafin da na ba ka mana.” Sai na ce, “Ai na riga na karance.” A hankali, sai ɗan’uwa Gardner ya ce, “To, bari dai mu yi nazarin wannan babi na farko.” Da ya soma nazarin, na yi mamaki cewa akwai abubuwa da yawa da ban fahimta ba. Ya sa na karanta nassosi da dama da aka ambata a littafin daga Littafi Mai Tsarki. A lokacin ne na soma koyon abubuwa game da Allah na gaskiya, Jehobah. Ɗan’uwa Gardner ya yi nazarin babobi guda uku na littafin da ni a safiyar. Ina kiransa da sunansa na farko, wato Jim. Daga lokacin, yana nazarin babobi uku da ni kowace ranar Alhamis da safe. Na ji daɗin nazarin da muka yi da shi sosai. Ba ƙaramin gata ba ne a ce ɗan’uwan da ya san Charles T. Russell sosai ne ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.

Bayan ’yan makonni, sai aka mai da ni mai shela da bai yi baftisma ba. Ɗan’uwa Jim ya taimaka mini in magance matsalolina da dama, kuma hakan ya haɗa da tsoron yin wa’azi gida-gida. (A. M. 20:20) Ina jin daɗin fita wa’azi tare da shi. Har zuwa yau, yin wa’azin bishara babban gata ne a gare ni. Ina farin ciki cewa ina aiki tare da Allah!—1 Kor. 3:9.

YADDA NA SOMA ƘAUNAR JEHOBAH

Yanzu barin in gaya maka wani abu game da kaina, wato yadda na soma ƙaunar Jehobah. (R. Yoh. 2:4) Ƙaunata ga Jehobah ta taimaka mini in jure tunanin abubuwa da suka faru a lokacin yaƙi da kuma wasu gwaji.—Isha. 65:17.

Ƙaunata ga Jehobah ta taimaka mini in jure tunanin abubuwa da suka faru a lokacin yaki da kuma wasu gwaji

Na yi baftisma a watan Yuli ta 1971 a taron Gunduma na “Divine Name” (Sunan Allah) da aka yi a filin wasan Yankee a Amirka

Na tuna da wata rana ta musamman a shekara ta 1971. Hakan ya faru ne jim kaɗan bayan iyayena sun kore ni daga gida. Mijin mahaifiyata ya ce, ba zai yarda Mashaidin Jehobah ya zauna a gidansa ba. A lokacin ba ni da isashen kuɗi. A asibitin da nake aiki, ana biya na kowane sati biyu, kuma na riga na sayi tufafi da albashina don in sami kayan fita wa’azin bishara. Ina da wata ajiyar kuɗi, amma yana wani banki a jihar Michigan, inda na girma. Saboda haka, na soma kwana a cikin motata. Nakan yi kwaskwarima kuma in yi gyaran fuska a ban ɗaki na gidajen mai.

A wannan lokacin, akwai ranar da na yi sammako zuwa Majami’ar Mulki kafin a soma taron fita wa’azi. Ban daɗe da tashi daga aiki ba. Na zauna a bayan Majami’ar Mulki inda ba wanda yake ganina, sai hankalina ya soma tashi saboda tunanin abubuwan da suka faru a yaƙin Vietnam, wato warin mutane da aka ƙone da jinin mutanen da suka jikkata. A cikin tunanina, ina ji da kuma ganin yadda matasa suke roƙona cewa: “Anya zan rayu kuwa? Zan rayu ne?” Na san cewa za su mutu, amma na yi iya ƙoƙarina don in ƙarfafa su kuma na ƙi nuna musu irin yanayin da suke ciki. Tunanin ya sa ni baƙin ciki sosai yayin da nake zaune a wurin.

Na yi iya ƙoƙarina in ci gaba da ƙaunar Jehobah kamar yadda na so shi tun farko, musamman lokacin da nake fuskantar matsaloli

Na yi addu’a yayin da hawaye suna zubowa daga idanuna. (Zab. 56:8) Sai na soma tunani sosai game da begen tashin matattu. Farat ɗaya, sai na tuna cewa: Ta wurin tashin matattu, Jehobah zai kawo ƙarshen dukan zub da jini da baƙin ciki da ni da wasu suka fuskanta. Allah zai ta da waɗannan samarin daga mutuwa kuma za su sami damar sanin gaskiya game da shi. (A. M. 24:15) A wannan lokacin ne ƙaunar Jehobah ta shiga zuciyata sosai kuma ta mamaye tunanina. Wannan rana ce ta musamman a gare ni. Tun daga wannan lokacin, na yi iya ƙoƙarina in ci gaba da ƙaunar Jehobah kamar yadda na so shi a wannan ranar, musamman lokacin da nake fuskantar matsaloli.

JEHOBAH YA NUNA MINI ALHERI

A yaƙi, mutane suna aikata mugunta, kuma ni ma na yi hakan. Amma yin bimbini a kan nassosi biyu da na fi so ya taimaka mini. Na farko shi ne Ru’ya ta Yohanna 12:10, 11, inda aka ce an yi nasara a kan Shaiɗan ba kawai ta wurin bishara ba, amma ta jinin Ɗan ragon. Na biyun ita ce Galatiyawa 2:20. Wannan ayar ta koya mini cewa Yesu Kristi ya mutu ‘domina.’ Jehobah ya marabce ni saboda jinin Yesu kuma ya yafe mini abubuwan da na yi. Sanin hakan ya taimaka mini in kasance da lamiri mai kyau kuma ya sa ina iya ƙoƙarina don in taimaka wa mutane su san gaskiya game da Jehobah, Allah mai jin kai!—Ibran. 9:14.

A duk lokacin da nake tunani game da rayuwata, ina godiya cewa Jehobah yana kula da ni a koyaushe. Alal misali, a ranar da Jim ya gano cewa ina kwana a cikin motata, sai ya tuntuɓi wata ’yar’uwa da take da gidan haya don ta taimaka. Hakika, Jehobah ya yi amfani da Jim da kuma wannan ’yar’uwar wajen yi min tanadin gida. Jehobah mai alheri ne sosai. Yana kula da masu bauta masa da aminci.

NUNA HIMMA DA SANIN YAKAMATA

A watan Mayu na shekara ta 1971, ya zama mini wajibi in je jihar Michigan don in yi wasu ayyuka. Kafin in bar ikilisiyar Delray Beach da ke jihar Florida, na cika bayan motata da littattafai sai na hau babbar hanyar da ta nufi arewa. Amma kafin in bar jihar Georgia, littattafan sun kare. Na yi wa’azin bisharar Mulki da ƙwazo a wurare dabam-dabam. Na tsaya don in yi wa’azi a kurkuku kuma na rarraba wa mutane warƙoƙi a gidajen wanka da kuma wuraren hutu. Har wa yau, ban san ko wa’azin da na yi a waɗannan wuraren ya yi tasiri ba.—1 Kor. 3:6, 7.

Amma a gaskiya lokacin da na soma sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki, ban iya magana da basira ba musamman ma sa’ad da nake yi wa dangina wa’azin bishara. Nakan yi musu wa’azi gaba gaɗi amma ba da basira ba. Ina ƙwazo saboda yadda na so Jehobah tun farko. Ina ƙaunar yayuna John da Ron kuma na yi musu wa’azi ko sun ƙi ko sun so. Daga baya na roƙi gafara don yadda na bi da su. Duk da haka, a kullum ina yin addu’a don Jehobah ya taimake su su san shi. Tun daga lokacin, Jehobah ya taimaka mini na san yadda zan yi wa’azi da kuma koya wa mutane gaskiya da basira.—Kol. 4:6.

WASU DA NA SO A RAYUWATA

Yayin da nake tunawa da ƙaunata ga Jehobah, ba na mantawa da wasu da na so a rayuwata. Ƙaunata ta biyu ita ce matata Susan. Na san cewa ina bukatar macen da za ta taimaka mini a yin wa’azin Mulki. Susan mace ce da take da dangantaka mai kyau da Jehobah. A lokacin da muke fita zance, na taɓa ziyarar ta a gidansu a birnin Cranston da ke Rhode Island. Tana zaune a ƙofar gida tana karanta Hasumiyar Tsaro. Abin da ya burge ni shi ne, tana karanta wani talifi da ba na nazari ba amma tana karanta nassosin da aka ambata a ciki daga Littafi Mai Tsarki. Sai na yi tunani, ‘Ai wannan ’yar’uwar tana son Jehobah sosai!’ Mun yi aure a watan Disamba 1971, kuma ina farin ciki cewa tun daga lokacin tana tallafa mini sosai. Duk da cewa Susan tana so na sosai, tana ƙaunar Jehobah fiye da kome kuma hakan yana burge ni.

Ni da matata Susan, da kuma ’ya’yanmu Paul da Jesse

Jehobah ya albarkace mu da yara biyu, Jesse da Paul, kuma Jehobah ya albarkace su yayin da suke girma. (1 Sam. 3:19) Ni da matata muna farin ciki don yaranmu sun so Jehobah da zuciya ɗaya. Har wa yau, suna bauta wa Jehobah don suna ƙaunarsa kamar yadda suka so shi tun farko. Kowannensu ya yi fiye da shekaru ashirin a hidima ta cikakken lokaci yanzu. Ƙari ga haka, ina alfahari da matan ’ya’yana Stephanie da Racquel, suna kamar ’ya’ya ne a gare ni. ’Ya’yana sun auri matan da suke ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu.—Afis. 6:6.

Ina gudanar da taron fita wa’azi a lokacin da nake hidimar mai kula mai ziyara

Bayan da na yi baftisma, na yi hidima na shekara 16 a Rhode Island, kuma na sami abokan kirki a wurin. Ba zan manta da dattawa da yawa masu hankali da muka yi hidima tare ba. Ƙari ga haka, ina godiya ga masu kula masu ziyara da yawa da suka kafa mini misali mai kyau. Gata ne a gareni in yi hidima tare da ’yan’uwa da suka ci gaba da ƙaunar Jehobah. A shekara ta 1987, mun ƙaura zuwa jihar North Carolina don mu yi hidima a inda ake bukatar masu shela kuma Jehobah ya ƙara albarkarmu da wasu abokan kirki. *

Mun ji daɗin yin wa’azi a yankunan da ba a yawan wa’azi

A watan Agusta 2002, an gayyace ni da matata mu yi hidima a Bethel da ke Patterson a Amirka. Na yi aiki a Sashen Kula da Hidima, matata kuma ta yi aiki a sashen wanki. Matata ta ji daɗin yin aiki a wurin. A watan Agusta na shekara ta 2005 ne na sami gatan zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Na ji kamar ban cancanci wannan matsayin ba. Matata ta yi fargaba saboda yawan aiki da kuma tafiye-tafiye da ke tattare da wannan gatan. Matata ba ta son shiga jirgin sama, amma muna yawan tafiya a cikin jirgin sama. Susan ta ce kalaman matan wasu membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun taimaka mata ta ƙudurta cewa za ta ci gaba da tallafa mini. Abin da ta yi ke nan kuma ina son ta don wannan halin.

Ina da hotuna da yawa a ofishina da suke da muhimmanci a gare ni! Suna tuna mini irin rayuwa mai kyau da na yi. Na sami albarka masu yawa a yin iya ƙoƙarina don in ci gaba da ƙaunar Jehobah kamar yadda na yi tun farko.

Shakatawa da iyalina yana sa ni farin ciki sosai

^ sakin layi na 31 Za a sami labarin hidima ta cikakken lokaci na Ɗan’uwa Morris a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2006, shafi na 16.