Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?​—⁠Sashe na I

Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?​—⁠Sashe na I

“A tsarkake sunanka.”—MAT. 6:9.

1. Ta yaya za mu yi amfani da addu’ar da aka ambata a Matta 6:9-13 sa’ad da muke wa’azi?

MUTANE da yawa sun haddace Addu’ar Ubangiji. Muna haɗuwa da mutane sa’ad da muke wa’azi gida-gida, mukan taimaka musu su fahimta cewa Mulkin Allah gwamnati ce ta zahiri da za ta kawo canje-canje masu kyau a duniya. Ko kuma mu nuna musu daga roƙo na farko cewa Allah yana da suna kuma ana bukata a tsarkake sunan.—Mat. 6:9.

2. Ta yaya muka san cewa Yesu bai so mu riƙa maimaita kalmomin addu’ar misali a duk lokacin da muke addu’a ba?

2 Shin Yesu yana nufin cewa mu riƙa maimaita wannan addu’a a kowane lokaci, kamar yadda mutane da yawa a Kiristendom suke yi? A’a. Kafin Yesu ya koyar da wannan addu’a, ya ce: “Garin yin addu’a . . . kada ku yi ta maimaitawa.” (Mat. 6:7) Jim kaɗan bayan haka, ya sake koyar da addu’ar, amma ya yi amfani da kalmomi dabam. (Luk. 11:1-4) Ta hakan, Yesu ya taimaka mana mu san abubuwan da ya kamata mu yi addu’a a kai da kuma tsarin da ya kamata mu bi sa’ad da muke addu’a. Shi ya sa ya dace da aka kira ta addu’ar misali.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika yayin da muke tattauna addu’ar misali?

3 Za mu bincika addu’ar misali a wannan talifin da kuma a na gaba. Yayin da muke yin hakan, ka tambayi kanka, ‘Ta yaya wannan addu’ar misali za ta taimaka mini in kyautata yadda nake addu’a? Mafi muhimmanci, ina yin rayuwar da ta jitu da wannan addu’ar kuwa?’

“UBANMU WANDA KE CIKIN SAMA”

4. Mene ne kalmar nan “Ubanmu” take tuna mana, kuma ta yaya Jehobah ya zama “Uba” ga waɗanda suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya?

4 Addu’ar nan da Yesu ya koya mana, addu’ar misali ce. Da yake ya ce mu kira Allah “Ubanmu,” hakan ya nuna cewa dukanmu ‘’yan’uwan’ juna ne kuma muna ƙaunar juna da gaske. (1 Bit. 2:17) Wannan ba ƙaramin gata ba ne! Jehobah ya ɗauke shafaffu a matsayin ’ya’yansa kuma ya ba su gatan zuwa sama, shi ya sa ya dace su kira Jehobah “Uba.” (Rom. 8:15-17) Kiristoci da suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya za su iya kiran Jehobah “Uba” don shi ne ya ba su rai kuma yana biyan bukatun dukan masu bauta masa da gaske. Waɗanda suke da begen zama a aljanna a duniya za su zama ’ya’yan Allah bayan sun zama kamilai kuma sun kasance da aminci a gwaji na ƙarshe.—Rom. 8:21; R. Yoh. 20:7, 8.

5, 6. Wace tarbiyya mai kyau ce iyaye za su iya ba wa yaransu, kuma yaya ya kamata kowane yaro ya ɗauki wannan tarbiyyar? (Ka duba hoton da ke shafi na 20.)

5 Iyayen da suke koya wa yaransu addu’a suna koya musu tarbiyya mai kyau don hakan zai sa yaran su ɗauki Jehobah a matsayin Ubansu wanda yake sama. Wani ɗan’uwa da yake yin hidimar mai kula da da’ira a Afirka ta kudu ya ce: “Muna addu’a tare da ’ya’yanmu mata kowane dare tun lokacin da aka haife su, sai dai idan ba na gida. ’Ya’yanmu mata sukan ce ba su tuna da ainihin kalmomin da muka yi amfani da su a waɗannan addu’o’in da muke yi daddare ba. Amma sun tuna da yadda yanayin yake yayin da muke addu’a cikin lumana da natsuwa. Da zarar sun soma koyan yadda ake yin addu’a, sai na ƙarfafa su su riƙa yin addu’a don na ji yadda suke bayyana ra’ayinsu da damuwarsu ga Jehobah. Hakan ya ba ni zarafin sanin abin yake zuciyarsu. Sai na taimaka musu su riƙa yin addu’a game da batutuwa masu muhimmanci da aka ambata a cikin addu’ar misali don addu’o’insu su kasance da ma’ana.”

6 Saboda haka, ’ya’yan wannan ɗan’uwan sun ci gaba da ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah yayin da suke girma. Yanzu haka sun yi aure kuma suna yin nufin Jehobah ta yin hidima ta cikakken lokaci tare da mazajensu. Iyaye, babu tarbiyyar da za ku ba ’ya’yanku da za ta fi koya musu yadda za su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Ko da yake, ya rage wa kowanne yaro ya ci gaba da ƙarfafa wannan dangantaka mai tamani. Hakan ya ƙunshi sanin ma’anar sunan Allah da kuma girmama sunan fiye da kome.—Zab. 5:11, 12; 91:14.

“A TSARKAKE SUNANKA”

7. Wane gata ne mutanen Allah suke da shi, kuma wane hakki ne yake kanmu?

7 Muna da gatan sanin sunan Allah da kuma na kasancewa “jama’a . . . domin sunansa.” (A. M. 15:14; Isha. 43:10) Mukan yi addu’a ga Ubanmu na sama cewa: ‘A tsarkake sunansa.’ Yin wannan addu’ar zai sa mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu guji faɗin ko kuma yin duk wani abin da zai ɓata sunansa mai tsarki. Ba zai dace mu yi kamar wasu a ƙarni na farko da ba sa aikata abin da suke wa’azinsa ba. Manzo Bulus ya ce game da su: “Gama a wurin al’ummai ana saɓon sunan Allah saboda ku.”—Rom. 2:21-24.

8, 9. Ka ba da misali a kan yadda Jehobah yake taimaka wa waɗanda suke so su tsarkake sunansa.

8 Burinmu ne mu tsarkake sunan Allah. Wata ’yar’uwa a ƙasar Norway da mijinta ya rasu ya bar ta da yaro ɗan shekara biyu, ta ce: Wannan mawuyacin lokaci ne a rayuwata. Nakan yi addu’a kullum, kusan kowane sa’a don in sami ƙarfin kasancewa da aminci da kuma guje wa duk wani abin da zai sa Shaiɗan ya zargi Jehobah. Ina son in tsarkake sunan Allah, kuma ina son ɗana ya sake ganin mahaifinsa a Aljanna.”—Mis. 27:11.

9 Shin Jehobah ya amsa addu’ar ta ne? Hakika. ’Yar’uwar ta ci gaba da yin tarayya da ’yan’uwa masu bi kuma hakan ya ƙarfafa ta. Shekaru biyar bayan haka, sai ta auri wani dattijo. Yanzu, ɗanta yana da shekara 20 kuma ya yi baftisma. “Ina farin ciki cewa mijina ya taimaka wajen tarbiyyartar da shi.”

10. Ta yaya Allah zai tsarkake sunansa?

10 Jehobah zai tsarkake sunansa sa’ad da ya halaka duk waɗanda suke gāba da sarautarsa. (Karanta Ezekiyel 38:22, 23.) A hankali, ’yan Adam za su zama kamilai. Muna marmarin ganin lokacin da dukan ’yan Adam da mala’iku za su tsarkake sunan Jehobah! Bayan haka, Ubanmu na sama mai ƙauna zai zama “kome” ga kowa.—1 Kor. 15:28.

“MULKINKA SHI ZO”

11, 12. Wane ƙarin haske ne Kiristocin gaskiya suka samu a shekara ta 1876?

11 Kafin Yesu ya je sama, manzanninsa sun tambaye shi cewa: “Ubangiji, a wannan lokaci ne ka ke mayar wa Isra’ila da mulki?” Amsar da Yesu ya bayar ta nuna cewa ba a wannan lokacin ba ne za su san lokacin da mulkin Allah zai soma sarauta. Ya gaya wa almajiransa cewa su mai da hankali ga yin wa’azin bishara mai muhimmanci. (Karanta Ayyukan Manzanni 1:6-8.) Duk da haka, Yesu ya koya wa mabiyansa cewa su sa rai ga zuwan Mulkin Allah. Shi ya sa tun daga lokacin, Kiristoci suna addu’a Mulkin ya zo.

12 Sa’ad da lokaci ya yi da Yesu zai soma sarauta daga sama, Jehobah ya taimaka wa mutanensa su gane shekarar da hakan zai faru. A shekara ta 1876, Charles Taze Russell ya rubuta wani talifi a cikin mujallar Bible Examiner. Jigon talifin shi ne: “Gentile Times: When Do They End?” (Yaushe Ne Lokatan Al’ummai Suka Ƙare?), kuma ya bayyana cewa 1914 shekara ce mai muhimmanci. Talifin ya bayyana cewa “lokatai guda bakwai” da aka ambata a littafin Daniyel ɗaya ne da “zamanan Al’ummai” da Yesu ya yi maganarsa. *Dan. 4:16; Luk. 21:24.

13. Mene ne ya faru a shekara 1914, kuma mene ne abubuwan da suke faruwa tun daga lokacin suka nuna?

13 A shekara ta 1914 an soma yaƙi a ƙasashen Turai, daga baya yaƙin ya shafi dukan duniya. Sa’ad da aka kawo ƙarshen yaƙin a shekara ta 1918, mutane da yawa sun yi fama da ƙarancin abinci. Ƙari ga haka, wata cuta da ake kira Spanish Influenza ta kashe mutane da yawa. Adadin mutane da cutar ta kashe ya wuce yawan mutanen da suka halaka a yaƙin. Wannan ‘alama’ ce da Yesu ya ce za ta sa a san cewa ya soma sarauta a matsayin sabon Sarkin duniya. (Mat. 24:3-8; Luk. 21:10, 11) Abubuwa da yawa da suka faru sun nuna cewa shekara ta 1914 ne aka ba Yesu ‘rawanin’ sarauta kuma ya fita yin yaƙi don ya gama cin “nasara.” (R. Yoh. 6:2) Ya yaƙi Shaiɗan da aljanunsa kuma ya koro su daga sama zuwa duniya. Tun daga lokacin, ’yan Adam sun shaida cikar wannan annabcin: “Kaiton duniya da teku: Domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gare shi, domin ya san sauran zarafinsa kaɗan ya rage.”—R. Yoh. 12:7-12.

14. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu yi addu’a cewa Mulkin Allah ya zo? (b) Wane gata ne muke da shi?

14 Annabcin da aka rubuta a Ru’ya ta Yohanna 12:7-12 ya sa mu fahimci dalilin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa a duniya tun lokacin da aka kafa Mulkin Allah. Yesu, Sarkin Mulkin Allah ya soma sarauta a sama ko da yake Shaiɗan yana mulki a duniya. Za mu ci gaba da yin addu’a cewa Mulkin Allah ya zo har sai lokacin da Yesu ya gama cin nasara kuma ya kawo ƙarshen mugunta a duniya. Ban da haka, wajibi ne mu ci gaba da yin rayuwar da ta jitu da wannan addu’ar ta wurin saka hannu a cikar sashe mafi muhimmanci na “alamar” ƙarshen zamani, wato wa’azin bishara. Yesu ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Mat. 24:14.

“ABIN DA KAKE SO, A YI SHI, CIKIN DUNIYA”

15, 16. Ta yaya za mu yi rayuwar da ta jitu da wannan roƙon cewa a yi nufin Allah a duniya?

15 Wajen shekaru 6,000 da suka shige, an yi nufin Allah a duniya. Shi ya sa bayan Jehobah ya gama halitta, ya ce kome “yana da kyau ƙwarai.” (Far. 1:31) Daga baya, Shaiɗan ya yi tawaye kuma tun daga lokacin, yawancin ’yan Adam ba sa yin nufin Allah a duniya. Amma muna godiya ga Allah cewa muna raye a lokacin da Shaidun Jehobah wajen miliyan takwas suna yin addu’a cewa a yi nufin Allah a duniya. Ƙari ga haka, suna yin rayuwar da ta jitu da addu’ar misali. Suna yin hakan ta yadda suke rayuwa da kuma ta yin wa’azin bishara da ƙwazo.

Shin kuna taimaka wa yaranku su yi rayuwar da ta jitu da roƙon nan cewa a yi nufin Allah a duniya? (Sakin layi na 16)

16 Alal misali, wata ’yar’uwa a Afirka da ta yi baftisma a shekara ta 1948 ta ce: “Ina roƙon Allah ya sa a taimaka wa mutane su zo ga saninsa kafin lokaci ya wuce. Ƙari ga haka, idan ina son in yi wa wani wa’azi, nakan roƙi Jehobah ya ba ni basira don saƙon ya motsa zuciyarsa. Kuma nakan yi addu’a Jehobah ya taimaka mana mu kula da duk wani mutum da ya karɓi saƙon bishara.” Hakan ya sa wannan ’yar’uwar da yanzu take da shekara 80 ta yi nasara a hidimarta kuma da taimakon ’yan’uwa, ta taimaka wa mutane da yawa su soma bauta wa Jehobah. Wataƙila ka san wasu da suka kafa misali mai kyau wajen yin nufin Allah da ƙwazo duk da cewa sun tsufa.—Karanta Filibiyawa 2:17.

17. Mene ne ra’ayinka game da abin da Jehobah zai yi don ya amsa addu’ar da muke yi cewa a yi nufinsa a duniya?

17 Za mu ci gaba da yin addu’a a yi nufin Allah har sai Mulkin Allah ya kawar da dukan magabtansa. Bayan haka, za mu shaida nufin Allah yana cika yayin da ake ta da biliyoyin mutane daga matattu don su yi rayuwa a aljanna a duniya. Yesu ya ce: ‘Kada ku yi mamakin wannan; gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryana, su fito.’ (Yoh. 5:28, 29) Babu shakka, za mu yi farin ciki sosai a lokacin da muke marabtar waɗanda aka ta da su daga matattu. Allah ‘zai share dukan hawaye kuma daga idanunmu.’ (R. Yoh. 21:4) Yawancin mutanen da za a ta da “marasa adalci” ne, wato waɗanda ba su sami damar sanin Jehobah da Yesu a lokacin da suka yi rayuwa a duniya ba. Za mu sami gatan taimaka wa waɗanda aka ta da su daga matattu su san nufin Jehobah don su sami damar yin rayuwa “har abada.”—A. M. 24:15; Yoh. 17:3.

18. Waɗanne bukatu ne suka fi muhimmanci ga ’yan Adam?

18 Sa’ad da Mulkin Allah ya zo, zai tsarkake sunan Allah kuma dukan ’yan Adam da mala’iku za su bauta wa Jehobah cikin haɗin kai. Waɗannan su ne bukatu mafi muhimmanci ga ’yan Adam. Saboda haka, Jehobah zai biya waɗannan bukatun sa’ad da ya amsa roƙe-roƙe guda uku da aka ambata a cikin addu’ar misali. Ban da haka, waɗanne bukatu huɗu ne kuma aka ambata a cikin addu’ar misali na Yesu? Za a tattauna su a talifi na gaba.