Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

“Jehobah Ya Kawo Ku Faransa don Ku Koyi Gaskiya”

“Jehobah Ya Kawo Ku Faransa don Ku Koyi Gaskiya”

SA’AD DA Antoine Skalecki yake yaro, yana da wani doki da yake hawa. Yana amfani da dokin wajen jigilar kwal a inda ake haƙawa. Kuma wurin yana da zurfin kafa 1,600. Mahaifinsa Antoine ya ji rauni sa’ad da wani ramin haƙar ya rushe, kuma hakan ya sa Antoine ya soma aiki a mahaƙar kuma yana aiki awa tara kowace rana. Akwai ranar da Antoine ya kusan rasa ransa sa’ad da ramin tonon kwal ya rushe a kansa.

Kayan aiki na masu haƙar ma’adinai ’yan Polan, mahaƙar ma’adinai inda Antoine Skalecki ya yi aiki a Dechy, kusa da Sin-le-Noble

Antoine yana cikin ɗimbin yara da wasu mutanen Polan da ke zama a Faransa suka haifa a tsakanin shekara ta 1920 da 1939. Me ya sa waɗannan mutanen Polan suka ƙaura zuwa Faransa? Sa’ad da Polan suka sami ’yancin kai bayan Yaƙin Duniya na ɗaya, ƙasar ta fuskanci matsalar yawan mutane. Amma kuma ƙasar Faransa ta rasa maza sama da miliyan ɗaya a yaƙin kuma ta yi ƙarancin ma’aikatan haƙar kwal. Saboda haka, gwamnatocin Faransa da na Polan sun ƙulla wata yarjejeniyar shige da fice a watan Satumba ta 1919. A shekara ta 1931 adadin ’yan Polan da ke zama a Faransa sun kai 507,800, kuma da yawa daga cikin su sun zauna a yankunan haƙar ma’adinai da ke arewacin ƙasar.

Waɗannan ’yan Polan suna da ƙwazo sosai. Ƙari ga haka, sun ƙaura zuwa ƙasar tare da al’adunsu da ya haɗa da ƙishin addini. Yanzu Antoine da ya yi shekara 90 ya ce: Kakana Joseph ya ɗauki Littafi Mai Tsarki da daraja sosai. Mahaifina ya gāji wannan halin. A ranar Lahadi, waɗannan ’yan Polan ma’aikatan da iyalansu sukan yi shiga mai kyau su je coci bisa ga al’adarsu. Amma hakan yana ɓata ran wasu ’yan ƙasar Faransa da suka tsani addini.

A yankin Nord-Pas-de-Calais ne mazauna da yawa ’yan Polan suka haɗu da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma wa’azi a yankin tun 1904. A shekara ta 1915 ne aka soma wallafa Hasumiyar Tsaro a yaren Polan kowane wata. An soma wallafa Awake! (a lokacin ana kiran mujallar The Golden Age) a yaren a shekara ta 1925. Iyalai da yawa sun amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki da ke waɗannan mujallun da kuma littafin nan The Harp of God a yaren Polan.

Iyalin Antoine sun haɗu da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ne ta wajen kawunsa da ya halarci taro da farko a shekara ta 1924. A shekarar ce Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka halarci babban taro na farko a yaren Polan. A cikin wata ɗaya, wakilin da ya zo daga babban hedkwata, Joseph F. Rutherford ya gayyace su zuwa wani taro kuma mutane 2,000 ne suka halarta. Yawancin mutanen da suka halarci taron ’yan Polan ne kuma hakan ya burge Ɗan’uwa Rutherford sosai, sai ya ce: “Jehobah ya kawo ku Faransa don ku koyi gaskiya. Yanzu, wajibi ne ku da yaranku ku taimaka wa mutanen Faransa! Ana bukatar a yi wa’azin bishara sosai kuma Jehobah zai samar da masu wa’azi don su yi hakan.”

Abin da Jehobah Allah ya yi ke nan! Waɗannan Kiristoci ’yan Polan sun yi wa’azi da zuciya ɗaya kamar yadda suka yi aiki a ma’adinan! Har wasu daga cikinsu sun koma ƙasarsu Polan don su yi wa’azin bishara. Waɗanda suka koma Polan don su yi wa’azi a wasu yankuna na ƙasar sun haɗa da Teofil Piaskowski da Szczepan Kosiak da kuma Jan Zabuda.

Amma, Shaidun Jehobah da yawa ’yan yaren Polan sun zauna a Faransa kuma suka ci-gaba da yin wa’azi da ƙwazo tare da ’yan’uwansu ’yan Faransa. A shekara ta 1926, an yi wani taro a yankin Sin-le-Noble kuma mutane 1,000 sun halarci sashen yaren Polan, mutane 300 suka halarci sashe na yaren Faransa. Wani rahoto da aka bayar a littafin nan, 1929 Yearbook of Jehovah’s Witnesses ya ce: “A shekarar ’yan’uwa 332 ’yan yaren Polan sun yi baftisma.” Kafin Yaƙin Duniya na Biyu, akwai ikilisiyoyi 84 a ƙasar Faransa kuma 32 daga ciki, ikilisiyoyin yaren Polan ne.

’Yan’uwa ’yan yaren Polan suna zuwa babban taro. “Shaidun Jehobah” shi ne aka rubuta a jikin motar

A shekara ta 1947 gwamnatin Polan ta yi kira ga ’yan ƙasar su koma kuma Shaidun Jehobah da yawa sun koma gida. Amma duk da haka, aikin da su da ’yan’uwansu ’yan Faransa suka yi ya sa an sami ƙarin masu shela a shekarar. Daga baya, wato daga shekara ta 1948 zuwa 1950 an sake samun ƙarin masu shela sosai! Sakamakon haka, ofishin Shaidun Jehobah na ƙasar Faransa ya naɗa masu kula da da’ira a karo na farko a shekara ta 1948 don a taimaka wa waɗannan sababbin masu shela. Huɗu daga cikin biyar da aka naɗa ’yan yaren Polan ne kuma ɗan’uwa Antoine Skalecki yana cikinsu.

Har ila, Shaidun Jehobah ’yan Polan da yawa da ke ƙasar Faransa suna amsa sunayen iyayensu da suka yi aiki tuƙuru a ma’adinai da kuma a wa’azin bishara. A yau, baƙin haure da yawa da ke ƙasar Faransa suna koyan gaskiya game da Jehobah. Ko da Shaidun sun koma ƙasarsu ko sun ci-gaba da zama a ƙasar waje, suna wa’azi da ƙwazo kamar ’yan’uwansu ’yan Polan da suka zauna a ƙasar Faransa.—Daga tarihinmu a ƙasar Faransa.