Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zuwa ga Masu Karatu

Zuwa ga Masu Karatu

An soma buga wannan mujallar da kake karantawa a shekara ta 1879. Tun daga lokacin, an sha canja fasalin wannan mujallar da yake abubuwa suna canjawa. (Duba hoton da ke sama.) Somawa da wannan fitowar, za ka lura cewa an yi wasu canje-canje a tsarin Hasumiyar Tsaro. Waɗanne canje-canje ke nan?

A ƙasashe da yawa, yawancin mutane suna jin daɗin yin karatu a Intane kuma ba shi da wuya a samu bayanai ta hakan. A cikin sauƙi, ana iya karanta wasu bayanan da sai ta Intane ne kaɗai za a same su. Akwai littattafai da mujallu da jaridu da yawa da ake karantawa ta Intane.

Saboda wannan ne muka canja fasalin dandalin www.ps8318.com don ya kasance da ban sha’awa kuma da sauƙin bincikawa. Waɗanda suka shiga dandalinmu za su iya karanta littattafai a harsuna sama da 430. Kuma somawa da wannan watan, wasu talifofi da a dā suke fitowa a mujallu da muke bugawa, yanzu za su riƙa fitowa a dandalinmu na Intane ne kaɗai kuma waɗanda suka shiga dandalin za su iya karantawa. *

Tun da yake talifofinmu da dama za su riƙa fitowa ne a Intane kaɗai, za a rage yawan shafuffukan Hasumiyar Tsaro na wa’azi daga 32 zuwa 16. Kuma an soma hakan ne da wannan mujallar. A yanzu haka, ana fassara Hasumiyar Tsaro cikin harsuna 204. Amma da wannan sabon tsarin, mai yiwuwa za a iya fassara mujallar cikin harsuna fiye da hakan.

Muna fata waɗannan gyare-gyaren za su taimaka wa mutane da yawa su ji saƙon Littafi Mai Tsarki don su sami ceto. Mun ƙudura za mu ci gaba da tanadar da bayanai masu ƙayatarwa ta wurin buga littattafai da kuma saka bayanai a Intane don ilimantar da mutane da suke son saƙon Littafi Mai Tsarki. Hakika, hakan zai sa su san ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

Waɗanda suka wallafa wannan mujallar

^ sakin layi na 5 Wasu cikin talifofi da za a riƙa samun su a Intane kaɗai su ne: “Don Matasa,” wanda tari ne na ayyukan yi da aka ɗauko daga labaran Littafi Mai Tsarki don matasa, da kuma “Abin da Na Koya Daga Littafi Mai Tsarki,” wanda shi ma tari ne na talifofi da aka shirya don iyaye su karanta tare da ’ya’yansu ’yan shekara uku zuwa ƙasa.