Yadda Za Ka Yi Manejin Kudin da Kake Samu
Kana fama ne da rashin isasshen kudi domin kudin da kake samu ya ragu ko tattalin arziki ya fadi? Annoba, ko bala’o’i, ko tashe-tashen hankula na siyasa ko kuma yaki, sukan sa tattalin arziki ya durkushe da wuri. Ko da yake rashin isasshen kudi yakan sa mutum ya soma damuwa, amma akwai wasu matakan da za su iya taimakawa, kuma ka’idodin Littafi Mai Tsarki ne.
1. Ka amince da sabon yanayin da ka tsinci kanka.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Na san yadda zan zauna . . . cikin yunwa ko cikin koshi, ko cikin rashi ko cikin samu.”—Filibiyawa 4:12.
Ko da ba ka da isasshen kudi yanzu, zai yiwu ka lallaba da abin da kake da shi. Idan ka yi saurin amincewa da yanayin da kuke ciki kuma ka yi gyara a yadda kuke kashe kudi, hakan zai taimaka wa kai da iyalinka ku iya jimre yanayin.
Ka bincika don ka san ko akwai tallafin da gwamnati ko wasu kungiyoyi suke bayarwa da za ka iya samu. Idan ka sami labari, ka dauki mataki da wuri domin irin damar nan tana saurin wucewa.
2. Ku yi shawara a matsayin iyali.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Idan babu shawara, shiri yakan lalace, amma tare da shawara mai yawa, akwai cin nasara.”—Karin Magana 15:22.
Ku zauna ku tattauna da matarka da kuma yaranka. In kun zauna kun yi magana da kyau, hakan zai taimaka wa kowa a iyalin ya fahimci halin da kuke ciki da kuma abin da zai yi don ya taimaka. Idan kowa ya koyi yadda zai yi manejin abin da kuke da shi, ba za ku barnatar da abin da kuke da shi ba kuma za ku kasance da dan kudi a hannu.
3. Ku kasafta yadda za ku kashe kudi.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Zai . . . zauna, ya yi lissafin abin da . . . zai ci.”—Luka 14:28.
Idan kudin da kake samuwa ya ragu, yana da muhimmanci ka san yadda kake kashe duka kudin da kake samuwa. Ka yi lissafin kudin da kake gani za ka samu a wata a yanayin da kake ciki yanzu. Sa’an nan ka rubuta abubuwan da kake saya a wata a yanzu da kuma yadda kake yin hakan, ko da ka san dole ka yi canji. Ka yi kokari ka yi ajiya don ka yi amfani da shi idan bukatar gaggawa ta taso.
Shawara: Idan kana rubuta abubuwan da kake saya, kar ka manta ka saka kananan abubuwan da kake saya. Mai yiwuwa ka yi mamakin kudin da kake kashewa a kan su. Alal misali, bayan da wani mutum ya yi lissafin kudin da yake kashewa, sai ya gano cewa kowace shekara, yana kashe darurruwan daloli a kan cingam!
4. Ka mai da hankali ga abin da kuka fi bukata.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ku iya zabar abin da ya fi kyau.”—Filibiyawa 1:10.
Ka gwada kudin da kuke samuwa da abubuwan da kuke saya, sa’an nan ka zabi abubuwan da za ku rage ko ku daina saya don kudin da kuke samuwa ya ishe ku. Ka lura da kudin da kuke kashewa a kan:
Tafiye-tafiye. Idan kana da motoci biyu za ka iya sayar da daya. Idan motarka mai tsada ce za ka iya sayarwa ka saya mai araha ko wanda ba zai rika cin kudi da yawa ba. Idan za ka je wani wuri, mai yiwuwa zai fi ka shiga motar haya ko babur, ko kuma ka je da keke. Za ka ma iya sayar da motarka.
Nishadi. Za ka iya daina kallon tashoshin talabijin da sai an sayi kati ko a biya kafin a same su. Ka nemi masu araha ko ma na kyauta.
Abubuwan da Kuke Amfani da Su Kullum. A matsayin iyali, ku tattauna yadda za ku rage kudin da kuke kashewa a kan ruwa da wutar lantarki da man fetur. Kashe wutar da ba a amfani da ita da kuma rage yawan ruwan da kuke wanka da shi zai iya rage kudin da kuke kashewa.
Abinci. Ku guji cin abinci a waje. Maimakon haka, ku dafa abinci a gida. Ku tsara abincin da za ku rika dafawa kuma ku saya da yawa idan zai yiwu. Ku duma abincin da ya rage ku ci. Ku rubuta abubuwan da za ku saya kafin ku je kasuwa don kar ku kama sayan duk abin da kuka gani kawai. Ku dinga sayan abincin da ake girbewa a wannan lokacin, don a yawancin lokuta su suka fi araha. Ku guji sayan kayan kwalama, wato, kayan kwadayin da ba sa gina jiki. Za ka iya yin lambu.
Kayan Sakawa. Kada ku dinga sayan kaya don kuna bin yayi, sai dai in wadanda kuke da su sun kode ko sun yage. Ku nemi kayan da ake fitarwa a karshen shekara a sayar da araha ko gwanjo masu kyau. Bayan kun wanke kayanku, ku shanya su a rana maimakon ku yi amfani da injin busar da kaya. Hakan zai rage muku kudin wuta.
Abubuwan da Kuke So Ku Saya a nan Gaba. Kafin ka saya wani abu ka tambayi kanka cewa: ‘Ina da kudin sayan wannan abin kuwa? Ina bukatarsa da gaske?’ Za ka iya kara jira kafin ka canja wasu kayan dakinka ko na’urorinka ko motarka? Idan kuma kana da kayan da ba ka amfani da su, za ka iya sayar da su? Hakan zai iya taimaka maka ka saukaka rayuwarka kuma ka kara samun kudi.
Shawara: Idan kudin da kake samuwa ya ragu sosai, hakan zai taimaka maka ka daina wasu abubuwa marar kyau da suka zama maka jiki, kamar shan taba da caca da yin tilis da giya. Wadannan abubuwan suna iya cinye ma mutum kudi. Idan ka daina, hakan zai sa ka iya manejin kudinka kuma ka inganta rayuwarka.
5. Ka yi kokari ka kusaci Allah.
Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Masu farin ciki ne wadanda suka san cewa suna bukatar kulla dangantaka da Allah.”—Matiyu 5:3, New World Translation.
Littafi Mai Tsarki ya ba mu shawara mai kyau, ya ce: “Hikima takan tsare mutum kamar yadda kudi yakan yi. Hikima takan kiyaye ran mai ita, wannan ita ce amfanin sani.” (Mai-Wa’azi 7:12) Bincika Littafi Mai Tsarki ne zai sa mu sami irin wannan hikimar. Shawarar Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa mutane da yawa su rage yawan damuwa a kan abin biyan bukata na yau da kullum.—Matiyu 6:31, 32.