WAƘA TA 31
Ka Bi Allah!
(Mikah 6:8)
-
1. Ka bi Allah da sauƙin kai,
Ka riƙa son gaskiya.
Ka riƙe aminci ga Allahnmu
Domin ya ƙarfafa ka.
Ka dogara da Kalmar Allah
Don kar a ruɗe ka.
Ka bar Allah ya bi da kai,
A cikin rayuwarka.
-
2. Ka bi Allah cikin tsarki,
Ka riƙa yin nagarta.
Ko da kana fuskantar jarraba,
Allah zai taimake ka.
Ka riƙa aikata nagarta
A duk rayuwarka.
In ka yi abubuwan nan,
Allahnmu zai bi da kai.
-
3. Ka bi Jehobah da murna
Domin yana ƙaunar ka.
Ka gode masa don alherinsa
Da kuma duk kyautarsa.
Ka bi Jehobah da daɗin rai,
Ka yabi sunansa.
Mutane za su san cewa
Kai bawan Jehobah ne.
(Ka kuma duba Far. 5:24; 6:9; Filib. 4:8; 1 Tim. 6:6-8.)