WAƘA TA 64
Mu Rika Yin Wa’azi da Farin Ciki
(Matta 13:1-23)
-
1. Yanzu muna lokacin girbi,
Domin shukarmu ta nuna.
Jehobah Ubanmu a sama,
Yana so mu yi wa’azi.
Yesu Kristi shi ne ja-gora,
Ya kafa misali mai kyau.
Muna murna sosai a koyaushe.
Don muna shelar bishara.
-
2. Muna yin wa’azin bishara
Don muna ƙaunar mutane.
Wa’azi na da muhimmanci
Domin ƙarshe yana tafe.
Jehobah na mana albarka,
Yana sa mu murna sosai.
Za mu riƙe aminci har ƙarshe
Muna wa’azi da himma.
(Ka kuma duba Mat. 24:13; 1 Kor. 3:9; 2 Tim. 4:2.)