Tafiya Zuwa Yankunan da Ke Kogin Maroni
Ko da yake ana yawan zirga-zirga a birni, mutane daga harsuna da kabilu da kuma kasashe dabam-dabam suna zama a dajin Amazon da ke Kudancin Amirka. Saboda haka, a watan Yuli 2017, wani rukunin Shaidun Jehobah guda 13 suka ziyarci yankunan da kogin Maroni ya ratsa cikinsu da na French Guiana. Mene ne burinsu? Domin su yada sakon Baibul ga mutanen da ke zama a yankunan.
Shiryen-shiryen Tafiyar
Wata guda kafin tafiyar da za ta dauki kwanaki 12, sai aka shirya wani taron da zai taimaka wa mutanen da za su yi tafiyar. Dan’uwa Winsley ya ce: “A taron ne aka gaya mana game da yanayin wurin da tarihin da kuma yadda za mu shirya kanmu domin tafiyar.” Sai matafiyan suka dauki kayan kwanciya da gidan sauro a cikin jakar da ruwa ba za ta iya shiga ba. Tafiyar nan za ta bukaci su shiga jirgin sama sau biyu da kuma yin amfani da kwale-kwale na sa’o’i da dama.
Yaya wadanda aka zabi su yi tafiyar suka ji game da hakan? Ko da yake Claude da Lissette sun kusan kai shekarun ritaya, sun yi farin ciki sosai da damar da aka ba su. Claude ya ce: “Na yi murna sosai, amma na ji tsoro kadan domin na ji cewa akwai wasu sassa na kogin da suke da hadari.” Lisette ita ma tana da nata damuwar, ta ce: “Na yi tunanin yadda zan iya magana da yarukan ’yan asalin Amirka.”
Wani dan’uwa mai suna Mickaël da ke cikin wadanda suka je wa’azin ya ce : “Ba mu san abubuwa sosai game da kabilar Wayana ba. Saboda haka, na yi bincike a Yanar gizo domin in koyi wasu kalmomi da kuma yadda zan yi gaisuwa a yarensu.”
Shirley wadda ta yi tafiyar tare da mijinta Johann, ta lissafta harsuna da ake yi a yanki. Ta ce: “Mun saukar da bidiyoyi daga jw.org a yawancin harsunan da ake yi a yankin, mun kuma sayi wani littafi na koyan yaren Wayana.
Mun Shiga Kasar ’Yan Asalin Amirka
A ranar Talata, 4 ga Yuli, sai rukunin ’yan’uwan suka hau jirgin sama a garin Saint-Laurent du Maroni zuwa Maripasoula, wani karamin gari da ke can cikin French Guiana.
A cikin kwanaki hudu rukunin suka yi wa’azi ga mazaunan kauyukan da ke tuddai na gefen kananan kogunan Maroni, sun yi amfani da kwale-kwale mai inji. “Mun ga cewa mutanen suna so su san gaskiya sosai,” in ji Roland, da ke cikin rukunin masu wa’azi. “Mutanen suna da tambayoyi da yawa kuma wasu a cikinsu sun so mu yi nazarin Baibul da su.”
A wani kauye, Johann da Shirley sun hadu da wasu ma’aurata da ba su jima da aure ba, kuma bai jima da wata ’yar’uwarsu ta kashe kanta ba. sai Johann ya ce: “Muka nuna masu bidiyo mai suna A Native American Finds His Creator, da ke a JW Broadcasting, bidiyon ya ratsa zuciyar ma’auratan har suka ba mu imel dinsu domin suna so mu ci gaba da tattaunawa da su.”
Kauye na karshe mafi nisa a bakin kogin da ’yan’uwan suka ziyarta shi ne Antécume Pata. A wurin, mai anguwan ya ba Shaidun da suka gaji tikis damar saka kayan kwanciyarsu a tsakiyar anguwa, kuma suka je suka yi wanka a rafi, inda kowa ke yi.
Daga wurin, rukunin suka je kauyen Twenké inda suka samu ’yan garin suna bakin cikin rasuwar wani. Eric, wanda yake cikin wadanda suka shirya tafiyar ya ce: “Mai anguwan ya ba mu izini mu zagaya anguwan domin mu ta’azantar da wadanda suke makoki. Kuma mai anguwan da iyalinsa sun yi farin ciki sosai sa’ad da muka karanta musu wasu nassosi a Baibul na yaren Wayana. Mun kuma nuna masu bidiyoyin da suke nuna tabbacin alkawarin tashin matattu.”
Mun Yi Gaba zuwa Grand-Santi da Apatou
Zango na gaba a tafiyar shi ne tafiya da jirgin sama na rabin awa daga Maripasoula zuwa Grant-Santi wani karamin gari a gangaren rafin. A ranar Talata da Laraba, matafiyar suka yi wa mutanen kauyen wa’azi. A ranar Alhamis, Shaidun suka sake wata tafiya na awa biyar da rabi a gangaren rafin Maroni zuwa kauyen Apatou.
A kusan rana ta karshe na tafiyar, sai rukunin suka ziyarce kauyukan da ake yaren Maroon, wadannan bayi ne na Afirka da aka kawo Amirka ta Kudu daga kasar Suriname a lokacin mulkin mallaka. Sai Shaidun suka gayyaci dukansu zuwa taro a wani babban tenti da aka kafa na musamman a dajin. “Mun yi farin ciki sosai lokacin da mutane da yawa suka halarci taron,” in ji Claude. “Da safe nan ne muka gayyace su!” Wani dan’uwa a rukunin mai suna Karsten, wanda farkon tafiyarsa ke nan zuwa gandun-daji, ya ba da jawabi mai jigo “Anya Wannan Rayuwa Shi Kenan Ne?” Mutane 91 daga kauyuka dabam-dabam ne suka halarci taron.
“A Shirye Muke Mu Sake Yin Hakan!”
Daga karshe matafiyan sun koma garin Saint-Laurent du Maroni. Dukansu sun yi farin ciki sosai saboda yadda mutanen garin suka saurari sakon, kuma sun karbi littattafai dabam-dabam da kallon bidiyoyi da yawa da Shaidun Jehobah suka wallafa.
Lisette ta ce: “Ina matukar farin ciki domin yin wannan tafiyar.” Cindy ma ta ce: “Idan zan iya samun dama yin haka kuma, zan karba da hannu biyu-biyu. Sai ka dandana za ka gane!”
Tafiyar ta sa wasu cikin ’yan’uwan su so komawa. “A shirye muke mu sake yin hakan!” in ji Mickaël. Winsley yakaura zuwa Saint-Laurent du Maroni. Claude da Lisette da suka ba shekaru 60 baya sun yanke shawara kaura zuwa Apatou.